An samu karin mutum 22 sun da suka kamu da Korona a jihar Osun

0

Gwamnatin jihar Osun ta bayyana cewa an samu karin mutum 22 da suka kamu da kwayoyin cutar Korona a jihar.

Kwamishinan kiwon lafiya Rafiu Isamotu ya sanar haka ranar Juma’a, a Osogbo.

Isamotu ya ce haka ya an gano wadannan mutane ne awa 24 bayan wasu mutum 17 sun kamu da cutar a jihar.

Ya ce ga dukan alamun cutar ta ci gaba da yaduwa ne a dalilin rashin kiyaye sharuddan guje wa kamuwa da ita da mutane ke yi a jihar.

Isamotu ya ce a dalilin haka gwamnati za ta sake saka dokar zaman gida dole a jihar idan aka ci gaba a haka.

“A ranar Alhamis mun sanar mutum 17 sun kamu da cutar sannan wasu kuma mutum 22 suka kara kamuwa da cutar a ranar Juma’a.

“An gano mutum 11 daga cikin su a kauyen Ede sauran an gano su a garin Osogbo.

“Muna kira ga mutane da su ci gaba da kiyaye sharuddan gujewa wa kamuwa da cutar Covid-19 domin har yanzu cutar na ci gaba da yaduwa.

Bisa ga sakamakon gwajin da jihar ke da shi na ranar 26 ga watan Yuni ya nuna cewa har yanzu mutane da dama na dauke da cutar a jihar.

Mutum 106 na kwance a asibiti, 47 sun warke sannan mutum biyar sun mutu.

Share.

game da Author