Wasu ma’aikatan kiwon lafiya dake aiki a asibitin FMC a Idi-Aba, Abeokuta, jihar Ogun sun kamu da cutar Korona.
Kakakin asibitin Segun Orisajo ya Sanar da haka ranar Juma’a.
Orisayo ya ce likitoci, ma’aikatan jinya da wani ma’aikacin asibitin Takwas suk kamu da cutar.
Wadannan ma’aikata sun kamu da cutar ne bayan cudanya da suka yi da wata jaririya ‘yar shekara biyu da ta kamu da cutar kuma ke samun kula a asibitin.
A kwanakin baya PREMIUM TIMES ta ruwaito yadda wata jaririya ‘yar shekaru biyu ta kamu da cutar Korona da a dalilin haka asibitin ta rufe sashen da ake kula da yara kanana.
An gano kwayoyin cutar a jikin wadannan ma’aikata ne a bayan gwajin daka yi wa duka ma’aikatan asibitin. Sakamakon gwajin ya nuna su takwas sun kamu.
A yanzu za akillace su na kwanaki 14 sannan a ci gaba da basu magani zuwa har su samu lafiya.
Sakamakon gwajin cutar da Hukumar NCDC ta fitar ranar Alhamis ya nuna cewa mutum 22,614 ne suka kamu da cutar a kasa Najeriya.
Sakamakon ya nuna cewa mutum 14,243 na da ita a jikin su wasu na kwance wasu kuma suna killace, 7,822 sun warke a kasar nan sannan mutum 549 sun mutu.
Har yanzu dai ana samun karin yawan mutanen da suka kamu da cutar a kasar nan babu kakkautawa.