Zakkar Dukiya, Zakkar Fidda Kai Da Sallar Idi A Musulunci, Daga Imam Murtadha Gusau

0

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai

Godiya ta tabbata ga Allah, Kyakkyawan karshe yana ga masu tsoron Allah, tsira da aminci su tabbata ga fiyayyen halitta, Manzon Allah (SAW) da iyalansa da Sahabbansa da wadanda suka bi su gaba dayan su, har zuwa ranar sakamako. Bayan haka:

Yaku ‘yan uwana Musulmi, lallai ku sani, hikimomin da yasa aka shar’anta Zakkah a Musulunci suna da yawa, yana daga cikin hikimar da ta sa aka shar’anta Zakkah ga wasu daga ciki kamar haka:

1. Tsarkake zukatan mutune daga cutar rowa, da nuna masu sharrin ta, da kuma sharrin makwadanci.

2. Yalwatawa ga talakawa, da toshe kofar mabukata da marasa shi.

3. Habbaka tsarin nan mai kyau na lura da bukatun al’ummah wanda rayuwa ta ginu a kansa, da samun rabo mai girma.

4. Tantance girman dukiyar da mawadata suke da ita, da wadda take hannun ‘yan kasuwa da masu hannu-da-shuni, domin kada a kebance dukiyar ta kadaitu a hannun wasu kebantattun mutane kawai, ko ta kasance tana kewayawa ne a tsakanin mawadata kawai.

• Ma’anar Zakkah

‘Yan uwa, Zakkah ita ce, “Wani gwargwado na dukiya da ya zama wajibi a fitar da shi na daga dukiyar, a kuma bayar da shi ga wadanda suka cancanta, idan dukiyar ta kai nisabi sananne da sharudda kebantattu.”

Ya ku jama’ah, Zakkah tsarkaka ce ga dukiya da kuma shi mai dukiyar. Allah madaukakin Sarki yace:

“(Ya Manzon Allah) karbi wani abu daga cikin dukiyar su a matsayin sadaka (Zakkah), wadda zata tsarkake su da zukatansu.” [Suratu Taubah, 103]

• Matsayin Zakkah a Musulunci

Ya ku jama’ah, ku sani, ita dai Zakkah daya ce daga cikin rukunan Musulunci guda biyar, wadda aka gwama ta tare da Sallah a wurare da dama a cikin Littafin Allah mai girma.

• Hukuncin Zakkah

Zakkah farillah ce wadda Allah ya wajabta ta akan dukkan Musulmi, wanda ya mallaki wani abu daga cikin dukiya tare da cika sharuddan ta. Allah ya wajabta ta a cikin littafin sa, sannan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yayi umarni da ayi riko da ita ga duk wanda ta wajaba akan shi, babba ne ko karami, namiji ko mace, mai lafiya ko mara lafiya, kai koda mahaukaci ne. Allah madaukakin Sarki yace:

“(Ya Manzon Allah) Ka karbi wani abu daga cikin dukiyar su a matsayin sadaka (zakkah)), wadda zata tsarkake su da zukatansu.” [Suratu Taubah, 103]

Kuma Allah Ta’ala yace:

“Ya ku wadanda suka yi imani! ku ciyar daga cikin dadadan abu da kuka nema kuma (ku ciyar) daga abinda mu ka fitar maku daga kasa…” [Suratu Bakarah, 268]

Kuma Allah mai girma da daukaka yace:

“Kuma ku tsaida Sallah ku bayar da Zakkah.” [Suratu Muzamil, 20]

Sannan Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a
gare shi yace:

“An gina Musulunci akan abubuwa guda biyar ne: Shaidawa babu abin bautawa da cancanta sai Allah, kuma Annabi Muhammad (SAW) Manzon Allah ne, da tsaida Sallah, da kuma bayar da Zakkah, da kuma ziyartar daki (wato aikin Hajji), da azumin Ramadan.” [Bukhari da Muslim]

• Dukiyar Da Ake Fitarwa Zakkah

Dukiyar da ya wajaba a cire mata Zakkah nau’uka hudu ce, sune kamar haka:

1. Kudi: Sune Zinari, Azurfa da kuma takardun kudi. Zakkah tana wajaba a zinari idan ya kai nauyin mithqali ashirin, to sai a cire daya bisa arba’in. Zakkah tana wajaba ne a azurfa, idan ta kai dirhami dari biyu, to ita ma sai a cire daya bisa arba’in, (wato a kasa dukiyar gida arba’in a fitar da daya). Ana kimanta takardun kudi da ake da su a yanzu (kamar Naira, Riyal, Dollar da sauran su) ana kimanta su da manyan kudi na asali da ake da su (wato Zinari da Azurfa) idan kudin da ake da shi sun kai nisabin daya daga cikin wadannan kudade biyu (wato zinari da azurfa) to Zakkah ta wajaba, kuma abinda za’a fitar shine daya cikin arba’in, idan shekara ta juyo masu.

2. Zakkar Dabbobi: Zakkah tana wajaba ga rakuma, shanu, da kuma awaki, idan sun kasance ana kiwon su ko mafi yawansu a sahara ko dazuzzuka halattattu har suka kai shekara. To idan shekara ta zagayo masu, kuma suka kai nisabi sai a fitar da zakkar su, saboda hantsa da kuma hayayyafa: dangane da irin dabbar sune kamar haka:

• Nisabin Awaki/Tumaki: Ana bayar da akuya daya idan sun kai 40 zuwa 120, Daga 121 zuwa 200 akuya biyu ake bayarwa, amma daga 201 zuwa sama, akuya uku, sa’annan a ko wanne dari akuya ce.

• Nisabin Shanu: Daga gwargwadon abin da aka kimanta sune 30 zuwa 39 za’a bayar da dan maraki ko maraka ‘yar shekara daya mace ko namiji. Daga 40 zuwa 59 za’a bayar da ‘yar shekara biyu. Daga 60 kuma ‘yar shekara daya guda biyu, haka a kowacce 30 ‘yar shekara daya a kuma kowacce 40 ‘yar shekara biyu.

• Nisabin Rakuma: Daga 5 zuwa 9 za’a bayar da akuya, daga kuma 10 zuwa 14 akuya biyu, sannan daga 15 zuwa 19 akuya uku, sannan kuma daga 20 zuwa 24 akuya hudu. Amma daga 25 zuwa 35 rakuma yar shekara daya, daga 36 zuwa 45 rakuma ‘yar shekara biyu. Amma daga 46 zuwa 60 rakuma ce mai shekaru uku za’a bayar. Daga 61 zuwa 75 rakuma mai shekaru hudu. Daga 76 zuwa 90 rakuma biyu masu shekaru uku, guda uku, sannan daga kowacce 40 za’a bayar da ‘yar shekara biyu, haka kuma a kowacce 50 ‘yar shekaru uku. Lallai ne game da dabbobi (Rakuma, shanu, awaki) wadanda aka rike su domin kasuwanci da habbaka (kamar na gidan gona) to idan shekara ta zagayo kansu za’a kimanta kimar su ne, sai a fitar da Zakkar a kimar, wato daya cikin arba’in (kamar Zakkar kudi kenan), idan kuma ba na kasuwanci ba ne, to ba’a bayar da Zakkah a kansu. Ba’a bayar da Zakkah a kowanne sai macen dabba. Kuma baya halatta a bada namiji sai a Zakkar shanu ko ta rakuma a maddadin mace, ko kuma idan nisabin duk maza ne.

3. Zakkar Amfanin Gona: Yana wajaba a bayar da Zakkar dukkan hatsi da ke fitowa daga kasa, haka kuma dukkanin ‘ya’yan itatuwa da ake aunawa ko ake ajiyewa kamar dabino da zabibi. Kuma ana lura da nisabi da kuma gwargodon da aka tsara idan sun kai sa’i 300 watau abin ya kai kimanin kilogram 624. Ana hada amfanin gona na shekara guda a hada sashin shi da sashi domin cika nisabi, idan ya kasance jinsi daya guda ne, kamar dabino mai nau’uka daban–daban a misali. Abun da za’a bayar na Zakkar ‘ya’yan itatuwa shine:

• Daya bisa goma ake cirewa ga abun da aka shayar ba tare da wahala ba kamar ruwan sama ne ya shayar da shi, (wato noman da aka yi cikin damina).

• Daya bisa ashirin idan aka shayar da shuka da wahala, kamar wanda aka shayar da ruwan rijiya da sauran su (wato kamar noman rani kenan).

• Kashi na uku cikin kashi hudun, daya bisa goma za’a cire ga abin da aka shayar a wani lokaci ruwan sama a wani lokacin kuma da ruwan rijiya.

Zakkah tana wajaba ne idan kayan gona suka nuna sosai, ko suka fara nuna.

Babu Zakkah ga abin da bai nuna ba na hatsi da kayan lambu, sai dai idan an tanada ne domin kasuwanci, to anan sai a cire daya bisa arba’in, idan shekara ta zagayo kuma bayan ta ya cika nisabi.

Abunda ake fitar wa daga cikin teku, kamar lu’ulu’u, murjani kifi, wannan babu Zakkah a kai game da su. Amma idan an tanada ne domin kasuwanci to za’a fitar da daya bisa arba’in idan shekara ta zagayo kuma in sun kai nisabi.

Tsintuwa, wato abinda nike nufi anan shine abinda aka binne a kasa, wato wanda ake hakowa a cikin kasa, to abinda yake wajibi da za’a fitar, kadan ne ko mai yawa, shine daya bisa biyar, wanda za’a bayar da shi ne a inda ake sarrafa arzikin kasa, sauran kuma na shi ne.

4. Zakkar kayan kasuwanci: Kayan kasuwanci su ne abinda aka ajiye domin saye-da-sayarwa saboda samun amfani na riba, kamar gidaje da motoci da dabbobi da abinci da abin sha da tufafi da kayan alatu da sauran ire-iren su. Kayan kasuwanci idan suka kai nisabi, kuma shekara ta zagayo to za’a cire abinda ya wajaba na Zakkah, sai a kimanta kaso mafi tsoka da za’a ba talakawa. Za’a cire daya bisa arba’in daga cikin kimar da aka yiwa asalin dukiyar. Ya halatta kuma a fitar da Zakkar kayan kudin daga asalin kayan ba daga kudin ba. Idan kuwa mutum yayi niyyar amfani da kayan kasuwancin ne a karan kansa (kamar motar shiga…) to babu Zakkah a cikin ta. Kananan dabbobi da aka haifa da riba da kasuwanci shekararsu shine shekarar asalin su idan ya kai nisabi.

• Sharuddan Wajabcin Zakkah

Zakkah tana wajaba ne akan dukkan wanda yake Da, Musulmi, Wanda ya mallaki nisabi, Cikakkiyar mallaka, Sannan kuma shekara ta kewayo a kan su. Wannan idan ba abinda aka tono a kasa ba ne.

• Fitar Da Zakkah

– Lokacin fitar da Zakkah: Yana wajaba a fitar da Zakkah da wuri kamar alwashi da kaffarah, domin sakakken umurni yana fa’idantar da ayi shi cikin gaggawa. Allah madaukakin Sarki yace:

“Ku bayar da Zakkah.” [Suratu Bakarah, 277]

Kuma ya samu ya jinkirta bayar da ita domin lokacin bukata ko wani dangi na kusa ko kuma makwabta.

– Hukucin wanda ba ya bayar Zakkah: A Musulunci, duk wanda yayi jayayya game da wajabcin Zakkah da gangan, kuma yana sane, to ya kafirta, koda kuwa ya bayar da Zakkar, domin ya karyata Allah madaukakin Sarki da kuma Manzon sa (SAW) da kuma ijma’in Malamai. Sai dai za’a nemi ya tuba, to idan ya tuba shikenan, idan kuma yaki, sai a kashe shi. Amma kuma wanda ya ki bayar da Zakkah don saboda rowa da sakaci, to za’a kwace ta da karfi daga hannun sa, kuma a raba wa mabukata, domin hawa kujerar na ki da yayi. Kananan yara da mahaukata waliyan su ne zasu cire masu Zakkah.

– Abun da aka sunnanta wurin fitar da Zakkah:

1. An sunnanta bayyanar da ita don a kawar da rudani da zargi.

2. Mutum za ya raba ta da kan shi, domin ya tabbatar ta isa ga mabukata.

3. Mutum za ya fadi wannan wurin rabawa, yace:

“Ya Allah ka sanya ta ganima, kada ka sanya ta bashi.”

4. Sannan ya kamata ga wanda aka ba wa yace:

“Allah ya baka lada akan abinda ka bayar, ya kuma sanya albarka a abunda da ya rage na dukiyar, ya kuma sanya shi ya zama mai tsarkakewa.”

5. An sunnanta ya bai wa talakawa na kusa da shi wadanda ciyar da su ba ta kan shi.

• Mutanen da ake bai wa Zakkah: Mutanen da ya halasta a bai wa Zakkah su takwas ne, sune kuma wandanda Allah madaukakin Sarki ya ambata da kan sa cewa:

“Lallai abin sani kawai ana bayar da Zakkah ne ga talakawa, miskinai, ma’aikatan Zakkah, da sabbin shiga addinin Musulunci don a lallashe su, da bayi don a fanshe su, da wanda ake bi bashi, da wanda yake wurin jihadi don daukaka kalmar Allah da matafiyi. Umurni ne daga Allah, kuma Allah mai cikakken sani ne, kuma gwani ne.” [Suratu Tauba, 60]

1. Talakawa: sune wadanda ba su da abun da zai wadatar dasu.

2. Miskinai: Sune wadanda ba su da abun da zai wadatar da su ko da rabi ne.

3. Ma’aikatan Zakkah: sune masu daukarta da kiyayeta idan babu masu yi.

4. Wadanda ake rarrashin zukatan su: sune shugabanni daga cikin mutanen su, wadanda suke son Musulunci ko son kamewa daga aukawa cikin sharrin su, ko suke son taimakawa don ci gaban addinin Musulunci.

5. Domin ‘yanta bayi: wadanda suka yi yarjejeniya zasu fanshi kansu daga wurin shugabannin su.

6. Wadanda ake bi bashi: nau’i biyu ne: i. Masu cin bashi don kawo maslaha tsakanin al’ummah. ii. Masu cin bashi don su tara amma ba su da abin biya.

7. Masu aiki don daukaka Kalmar Allah: sune wadanda suke yaki don tabbatar da Kalmar Allah da kuma Malamai masu karantar da addini da aikin Da’awah zuwa ga hanyar Allah.

8. Matafiyi: shine matafiyi wanda guzurin sa ya yanke, kuma bai samu abin komawa gida ba.

• Zakkar Fidda Kai

1. Hikimar da tasa ake yin ta: Daga cikin hikimar da tasa ake yin Zakkar fidda kai ita ce: Ta na tsarkake zukatan masu azumi ne daga abinda suka aikata marar kyau, kamar yadda ta ke wadatarwa ce ga talakawa da miskinai daga barin roko da bara a ranar idi.

2. Gwargodon abin da ake cirewa da irin abincin da ake fitarwa: Gwargodon ta shine sa’i daya. Sa’i daya kuma shine mudun Nabiyi hudu, kuma ana kadara sa’i da ‘kilo wat’ uku. Ana kuma fitar wa ne daga mafi rinjayen abincin da mutanen garin suka fi ci a wannan lokacin, kamar su alkama, dabino, shinkafa, zabib da sauran su.

3. Lokacin da aka wajabta fitar da ita: Zakkar fidda kai ta na wajaba ne da zarar daren idi ya shiga (wato da zarar an ga watan karamar Sallah (Shawwal)). Lokacin bayarwa kuma yana halasta ne tun kafin ranar Sallah da kwana daya ko biyu, domin aikin Abdullahi Dan Umar Allah ya kara masu yarda da ya nuna hakan. Kuma lokacin bayarwar da yafi shine daga fitowar alfijir na ranar idi har zuwa dab da Sallar idi, domin umurnin Manzon Allah (SAW) da yayi na a bayar da ita ga mutane kafin fita zuwa Sallah.

4. Wadanda Zakkar fidda kai ta wajaba a kansu: Ita Zakkar fidda kai tana wajaba ne ga dukkan mutumin da yake Musulmi, Da, ko Bawa, mace ko namiji, babba ko karami, wanda Allah ya azurta da abincin da ya rage bayan na wuni da dare, kuma yana halasta a fitar wa da Dan da yake cikin mahaifa, wato cikin mahaifiyar sa.

5. Wadanda ake ba Zakkah: Zakkar kono (wato Zakkar fidda kai), ana bayar da ita ne ga duk wanda ya cancanci a ba shi sauran Zakkah ta dukiya, daga cikin mutane takwas din nan, amma talakawa da miskinai sun fi cancanta daga sauran da aka ambata, domin fadin Ma’aikin Allah (SAW):

“Ku wadatar da su daga barin roko na wannan ranar (Ranar Idi).”

• Sallar Idi

1. Hikimar da ke cikin Shar’anta Sallar Idi: Sallar idi na daga cikin alamomin addinin Musulunci bayyanannu wadanda Allah ya kebance alummar Annabi Muhammad (SAW) da su, wurin tabbatar da godiya ga Allah majibinci akan kammala ibadar azumin watan Ramadan (A karamar Sallah kenan), da kuma ziyartar dakin Allah mai alfarma da nufin ibadar aikin Hajji (A babbar Sallah kenan). Kamar yadda ya kasance a cikin idi, akwai kira zuwa ga tausayi da jin kai tsakanin al’ummar Musulmi da haduwar su a wuri daya, da kuma daidaita zukata.

2. Hukuncin Sallar Idi: Sallar idi farillah ce ta kifaya wadda idan wasu suka yi sun dauke wa wasu. Manzon Allah (SAW) da Halifofin bayan sa sun kasance suna aikata ta. Kuma ita Sunnah ce mai karfi akan kowane Musulmi, namiji ko mace, kuma an shar’anta ta ga mazauna ban da matafiya. Sannan kuma ita ba farillah bace da idan mutum bai yi ba yayi zunubi ko ya sabawa Allah. Sannan idan aka dakatar da Sallar idi a cikin cunkoson jama’ah, aka sanar da cewa kowa yayi Sallar idin sa a gida, tare da iyalan sa, sanadiyyar wata cuta ko wata lalura ko wata annoba, to ba’a yi laifi ba kuma ba’a sabawa Allah ba, ba’a yi zunubi ba, kuma wallahi ba’a yi kuskure ba. Duk kuma wanda yace an sabawa Allah idan ba’a yi Sallar idi ba saboda wata lalura, to yazo muna da hujja ko dalili!

3. Sharuddan Sallar Idi: Shuruddan Sallar idi kamar juma’ah ce, sai dai ban da huduba, hudubobi biyu, domin su Sunnah ne a Sallar idi, kuma ana yin su ne bayan Sallah, ita kuma juma’ah kafin Sallah.

4. Lokacin Sallar idi: Lokacin ta shine, daga dagowar rana da safe gwargwadon tsawon mashi, har zuwa zawali (wato gushewar rana daga tsakiya). Idan ba’a san da idi ba har bayan zawali sai a Sallace ta gobe a matsayin ramako na lokacin ta.

5. Yadda ake yin Sallar Idi: Sallar idi raka’ah biyu ce, domin fadin Sayyidinah Umar (RA):

“Sallar Fitri (wato karamar Sallah) da Sallar Adha (wato babbar Sallah) raka’o’i biyu ne cikakku ba tare da ragi ko kari ba, akan harshen Annabin ku (SAW), duk wanda ya kirkiro wani abu to ya tabe.” [Imam Ahmad]

Ana yin Sallar idi ne kafin ayi hudubah. Za’a yi kabbara a raka’ar farko bayan kabbarar harama, kuma kafin ta’awuzi kabbarori shida. A raka’ah ta biyu kuma za’a yi kabbarah kafin karatu sau biyar. Kuma duk wanda zai yi Sallar idi a gida da shi da iyalin sa saboda lalurar annobar korona, to babu laifi, hakan yayi daidai. Kuma yadda ake yin Sallar idi a filin idi, nafilah, raka’ah biyu, haka zai yi ta a gidan sa babu wani babanci, huduba ce kawai ba zai yi ba. Kuma Sallar idin sa tayi, sannan wallahi duk duniya, babu wani malami da ya isa yace wadanda suka yi Sallar idi a filin idi, cikin jama’ah, sun fi shi lada ko wani matsayi. Wannan sam ba gaskiya bane. Allah yasa mu dace, kuma ya yaye muna wannan annobar ta korona, amin.

6. Wurin da ake yin Sallar idi: Asali ana yin Sallar idi a fili ne, idan babu wata matsala ko wata lalura daga cikin lalurori. Amma kuma a sani, ya halasta ayi ta a cikin Masallaci ko a gida idan bukatar hakan ta kama. Misali, a irin halin da muka samu kan mu a ciki yau, sanadiyyar lalurar annobar korona da ta ke addabar duniya baki daya. Duk wadannan mutane da suke ta kururuwa da ihun banza, suna cewa wai lallai, dole-dole sai an yi Sallar idi a cikin cunkoson jama’ah, yadda aka saba yi, wannan suna yi ne kawai saboda jahilci ko son zuciyar su. Kasashen Musulmi irin Saudiyyah, Masar, Indonesiya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Morocco da sauran su, ba mu fi su addini ba, amma wallahi tuni Malaman kasashen suka yi taro, suka ba da fatawar cewa, kowa yayi Sallar idin sa a gidan sa. Kuma shugabannin wadannan kasashe tuni sun zartar da hukunci akan wannan fatawa ta wadannan Malamai. Amma mu anan Najeriya abun ba haka bane, mu komai sai mun siyasantar da shi, ko mu nuna cewa mu jahilai ne, ko kuma mu bi son zuciyar mu. Ina rokon Allah ya kare mu daga sharrin jahilci da bin son zuciya, amin.

7. Sunnonin Sallar Idi: An sunnanta yin kabarbari ba tare da kayyade cewa sai bayan idar da Salloli ba, da kuma bayyanar da kabarbarin tun a daren Sallah din, saboda fadin Allah mai girma da daukaka:

“Kuma domin ku cika lissafi, kuma ku girmama Allah (wato ku yi masa kabarbari) akan abinda ya shiryar da ku.” [Suratu Bakarah, 185]

Kuma Imamu Ahmad yace:

“Abdullahi Dan Umar Allah ya kara masu yarda, ya kasance yana kabarbari a duk idin guda biyu.”

Kuma game da goman farko na Zul-Hijjah, sai Allah madaukakin Sarki yace:

“Kuma su ambaci Allah a wadansu kwanuka sanannu.” [Suratu Hajji, 28]

Amma kabarbari da aka kayyade sune wadanda suka kebanci bayan Salloli, wannan ko ya kebanci idin babbar Sallah ne kadai, ban da karamar Sallah. Sai a fara ga wanda baya wurin aikin Hajji, daga Sallar asuba ta ranar arafah, har zuwa karshen kwanakin babbar Sallah.

Sannan an so mamu ya isa Masallacin idi da wuri kafin zuwan liman, amma idan har shugabanni sun yarda ayi Sallar a filin idi kamar yadda aka saba, amma shi liman sai ya jinkirta, ba zai isa wurin Sallar ba har sai lokacin ta yayi. Kuma an so mai tafiya Sallar idi yayi tsafta domin halartar ta, ya kuma sanya sabbin tufafi ko mafiya kyawun tufafinsa, kuma ya sanya turare, kuma mata kada su bayyanar da adonsu, kuma kar su sanya turare.

8. Sunnonin idi: An so a gabatar da Sallar idin babbar Sallah da wuri, kuma a jinkirta ta a karamar Sallah. Kuma an Sunnanta cin abinci kafin a fita a karamar Sallah, kodai aci dabino, da kuma kame baki daga barin cin abinci a lokacin babbar Sallah, domin a fara ci daga abin da aka yanka na layyah.

Wallahu ‘Alamu. Allah yasa mu dace, amin.

Ina rokon Allah ya kyauta, kuma ya kawo muna mafita ta alkhairi a dukkanin al’amurran mu, amin.

Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.

Share.

game da Author