Coronavirus ta darkako Afrika gadan-gadan, ta kama sama da mutum 90,000 -WHO

0

Alamomi na nuna cewa Coronavirus ta karkato gadan-gadan, yayin da kididdigar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ta bayyana cewa wadanda suka kamu da cutar Coronavirus a Afrika sun zarce 90,000.

Ofishin Afrika na WHO da ke Brazzaville, babban birnin kasar Congo ne ya fitar da wannan adadin ranar 20 Ga Mayu.

Har yau dai Afrika ta Kudu ce mai mutum 17,200, sai Aljeriya ke gaba wajen yawan masu cutar, mutum 7,377. Najeriya ce ta uku mai mutum 6,401. Ghana ce ta hudu da mutum 6,096.

PREMIUM TIMES ta wallafa a ranar Talata cewa Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya (WHO) ta bayyana cewa ya zuwa ranar Talata, 19 Ga Mayu, wadanda suka kamu da Coronavirus a Afrika sun zarce mutum 86,000.

Idan ba a manta ba, ranar 11 Ga Maris ne WHO ta bayyana cewa kasashe kowace ta yi ta kan ta, domin cutar Coronavirus ta zama mummunar annoba.

A wancan lokacin wadanda cutar ta kama a duniya ba su kai mutum 10,000.

Amma ya zuwa yanzu cutar ta kama sama da mutum milyan 4.5 a duniya, kuma ta kashe sama da mutum 300,000.

Kwanan baya WHO ta ce idan ba a dauki mataki ba, cutar za ta iya kama mutum milyan 250 a Afrika.

Safiyar Talatar nan WHO ta nuna fargabar cewa cutar za ta sake mamaye duniya fiye da halin da ake ciki a yanzu idan kasashe suka ci gaba da gaggawar janye dokar zaman gida dole da ta tafiye-tafiye, ba tare da sun yi kwakkwaran daukar matakai ba.

A bangaren Afrika, WHO ta bayyana jerin kasashen da aka fi kamuwa da cutar Coronavirus kamar haka:

Afrika ta Kudu: 16,432
Aljeriya: 7,201
Najeriya: 6,175
Ghana: 5,735
Kamaru: 3,529

Kasashen Losotho. Tsibirin Comoros da Tsibirin Seychelles ne kasashen da ke da karancin wadanda suka kamu da cutar.

Losotho: 1
Comoros: 11
Seychelles: 11.

Share.

game da Author