Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin mutum 284 da suka kamu da cutar Coronavirus a kasar nan ranar Laraba.
Alkaluman da NCDC ta fitar ranar Laraba, Jihar Legas ta samu karin mutum 199, 26-Ribas, 19-Oyo, 8-FCT, 8-Borno, 7-Plateau, 6-Jigawa
5-Kano, 2-Abia, 1-Ekiti, 1-Delta, 1-Kwara, 1-Taraba.
Yanzu mutum 6677 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 1840 sun warke, 200 sun mutu.
Idan ba a manta ba shugaban Kwamitin Shugaban Kasa Kan Dakile Yaduwar Korona, kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya bayyana cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da tswaita dokar hana zirga-zirga da mako biyu.
Mustapha ya shaida haka a jawabin mako-mako da kwamitin sa ke yi duk ranar litini ga manema Labarai.
” Tsawaita wannan doka ya zama dole domin har yanzu cutar Korona na ci gaba da yaduwa a kasar nan. Ba zai yiwu a yi gangancin janye dokar hana zirga-zirga ba yanzu.
” Dole a tsawaita domin a samu damar ci gaba da aikin dakile yaduwar cutar kamar yadda kwamitinsa ke yi da sauran ma’aikatan da aikin ya shafa.
Discussion about this post