Allah ya kiyayemu. Allah ya kawomu wani lokaci da ake yin rashin hankali da sunan wayewa. Dama Annabi (SAW) yace za a zo lokacin da idan Bayahude ya shiga ramin damo sai an samu wani musulmin ya shiga da sunan kwaikwayo. Allah ya tsaremu. Gashi nan kuwa muna gani. Hauka iri iri. Daga wannan sai wannan.
Masifa ce tazo wa wasu mazan marasa kishin matansu. Mace ta kunna wakar Hausa a gidanta tana girgizawa mijinta jiki suna turawa a “social media”. Duk wanda yake da “data” zai iya kalla har yayi zinar ido da matarka ya biya buqata. Haka abun yake. “Rabo daga Allah tsuntsu daga sama gasashshe” inji Bahaushe.
Annabi (SAW) yace, mutumin da baya kishin matarsa sunansa “Addiyus” wanda kanshin aljanna ma ba zai ji ba. Idan ba kauyenci ba, matarka ce fa. Idan zaku kai karshen “lockdown” kuna rawa a gida da ita ina ruwan wani.
Matarka ce ta sunnah. Idan kana so zaka iya zama kamar ALI NUHU, ita matar sai ta zama kamar RAHMA SADAU. Shi kuma gidan sai ka mayar dashi kamar KANNYWOOD. Zaman lafiya ne yake kawo nishadi.
Amma nunawa duniya da ake yi rashin kishi ne saboda nema ake yi a mayar da matan aure kamar wasu “ARTISTS”. Abun ya zama yayi yanzu, kuma shaidan ne yake tinzira mutane. Sai kun yi da gaske Wallahi.
Duk sanda dan Adam ya sauka daga layin addininsa da kuma al’adarsa wacce bata sa6awa addini ba, ya shiga uku ya lalace. Don komai ma zai iya yi tunda ya rasa kan-gado.
Kowacce al’umma tana da abinda ake kiransa da “values” Sune suke saita kowane mutum a cikin wannan alqarya. Musulmi yana da nasa, hakazalika kirista ma yana da nasa. Kuma Bahaushe yace, “Kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi.”
Musulunci yafi kowa wayewa, don shi yace mu yi kishin matan mu. Kuma nafsi yace kada mu bar matanmu su dinga shiga irin ta jahiliyar farko. To gasu nan yanzu a sadaka ana ganin rusarsu a wayoyin mutane ana sha’awarsu.
Allah ya shiryar damu.