Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami, ya bayyana cewa Dokokin Karfin Ikon da Shugaba Muhammadu Buhari ke sa wa hannu kwanan nan, su na kara wa wasu dokokin da Majalisar Tarayya su ka yi ne, domin kara karfin yadda ayyukan hukumomin gwamnati za su rika tafiya kafada da kafada da juna.
Kakakin Yada Labarai na Malami, mai suna Umar Gwandu ne ya bayyana haka, kamar yadda ya ce Malami ya shaida a wata tattaunawa da wani gidan talbijin ya yi da shi.
Ya ce kafa dokokin karfin iko da Shugaba Buhari ya yi za su kara jaddada bon tafarki da tsarin doka, ka’idar aiki, tilasta bin ka’ida da kuma sa-ido a dukkan hukumomin tarayya.
Ya ce Dokar Karfin Ikon Shugaban Kasa ta na da muhimmancin tilasta wanzar dokokin Majalisar Tarayya, kamar yadda tsarin mulki sashe na 121 (3) ta bai wa Bangaren Zartaswa da kuma Bangaren Shari’a karfin ‘yanci.
Ya ce dokokin na kara jaddada yadda kowane bangaren hukumomin gwamnati zai nabba’a wajen tafiyar da ayyukan hukumar a kan ka’ida.
“Duk da ana ganin kamar dokar karfin iko ce, amma idan Shugaban Kasa na son jaddada dokar a kan jihar da ta ki bin umarnin dokar wajen bayar da kudaden cin gashin kai ga Majalisar Jiha da bangaren shari’a, to sai ya nemi hadin kan Ofishin Akanta Janar tukunna.”
“Dokar Karfin Ikon Shugaban Kasa mai lamba 10, ta na kara jaddada karfin ikon dokar da ta wajabta cin gashin kan Majalisun Jihohi ne da bangaren shari’a na jihohi.” Inji Malami.