Yadda Buhari ya yi wa ‘yan sanda garambawul, ya kirkiro wasu rundunonin shiyya

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da yi wa Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Garambawul, tare da kirkiro Jami’an Leken Asiri na Musamman.

Wadannan bangaren leken asirin musamman, an cire su daban daga bangaren bincike na CID.

Musamman kuma za a kafa wasu ‘yan sandan shiyya-shiyya a bangarori biyar. Wadannan wasu ne daga cikin garambawul din da Buhari ya amince a yi.

Wannan bayani ya fito ne daga cikin wata sanarwa da Sufero Janar na Kasa, Muhammad Adamu ya sa wa hannu da kan sa.

Shugaban Kasa shi ne Shugaban Majalisar Hukumar Gudanarwar ‘Yan Sanda, wadda kowane gwamna 36 na kasar nan su na ciki. Zai iya amimcewa da wannan garambawul din, amma duk da haka, sai ya nemi yardar sauran mambobin majalisar hukumar ‘yan sandan, ta hanyar gayyatar su taro, inda za su amince masa da zartas da garamnawul din.

“Wannan garambawul zai kara samar da gagarimin aikin kula da sa-ido da leken asirin duk wata barazanar masu aikata muggan laifuka a cikin al’umma.

Wannan sabon sashe ko bangare na masu leken asiri, shi ne cikon bangare na takwas na ‘yan sandan Najeriya.

Kafin kirkiro shi dai akwai bangarori shida na hukumar rundunonin ‘yan sandan Najeriya.

Sannan kuma Buhari ya kara raba sashen CID, inda ya bude shiyya biyu, daya a Enugu, daya kuma a Gombe.

Sabbin kwamand na shiyya da aka kirkiro

1 – Ondo da Ekiti mai hedikwata a Ondo

2 – Enugu, Ebonyi da Anambra mai hedikwata a Ukpo- Dunokopia

3 – Bayelsa da Ribas, mai hedikwata a Yenegoa

4 – Yobe da Barno mai hedikwata a Maiduguri

5 – Kaduna da Katsina mai hedikwata a Katsina.

Share.

game da Author