Mutum 150 suka mutu, kuma ba Coronavirus ba ce ta kashe su – Gwamna Bala

0

Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya ce mutum 150 da suka mutu a jihar Bauchi ba Coronavirus bace ta kashe su.

Mohammed ya ce an samu tabbacin cewa mutum daya daga cikin su ne ya mutu a dalilin Coronavirus.

A wata wasika da tsohon dan majalisar tarayya Ibrahim Baba ya aika wa shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi kira ga gwamnati da ta gaggauta kawo wa jihar dauki cewa mutum 300 sun mutu a dalilin kamuwa da coronavirus a jihar.

A wasikar, Baba ya yi bayanin cewa mutum 100 sun mutu a dalilin kamuwa da coronavirus a garin Azare da kewaye a cikin sati daya.

Ya kuma ce gidajen jaridu ba su buga labarin abin dake faruwa ba saboda sun fi maida hankali wajen dauko rahotannindaga manyan garuruwa da birane.

Baba ya yi kira ga Buhari da ya aika da hukumar NCDC da kayan aiki da na tallafi zuwa garin Azare domin a duba sannan a tabbatar da abinda ke faruwa.

Bayan haka wani dan jihar mai suna Musa Azare ya rubuta wa gwamna Mohammed wasika kan mutuwar da mutane ke yi a jihar.

Musa Azare ya ce a ranar Alhamis din da ya gabata ya samu labarin cewa an haka ramuka 301 domin bizne mutanen da suka rasu a Azare a tsakanin kwanaki 14 da suka wuce. “Ina da majiya wacce ta tabbatar Mun da wannan labari.

Azare ya ce abin da ya fi ci masa tuwo a kwarya shine yadda mutane ke bizne wadanda suka mutu ba tare da sun nemi kariya domin gujewa wa kamuwa da cutar ba.

Mutane kalilan ne suka mutu

A ranar Asabar ne mataimakin gwamna kuma shugaban kwamitin yaki da cutar na jihar Bauchi Baba Tela ya karyata yawan mutanen da ake cewa sun mutu a jihar.

Tela ya ce tabas mutane sun mutu amma ba su kai yawan da ake ta yayadawa ba.

“Wasu sun ce mutum biyar ne suka mutu wasu sun ce mutum 300 ne suka mutu.

“Hakan dai ya sa na je garin Azare inda na tattauna da masu bizne mutane a makabarta. Kuma sun ce da gaske an yi ta mace-mace amma kamar yadda aka saba ne ba kamar yadda ake ta yayadawa ba wai coronavirus ce.” Inji Baba Tela

Dokar Zaman Gida Dole

Gwamna Bala Mohammed ya saka dokar hana walwala na awa 24 a kananan hukumomin Azare, Giade da Zaki na tsawon kwanaki 10.

Mohammed ya ce ya saka dokar ne saboda barkewar coronavirus a wadannan Kananan hukumomi.

Kuma ya ce wasu wasu cututtukan ne ya kashe su ba coronavirus ba.

Share.

game da Author