CORONAVIRUS: Saudiyya ta soke tallafin wata-wata ga ‘yan kasa, ta nunka harajin ‘VAT’ nunki uku

0

Kasar Saudiyya ta bayyana cewa ta nunka harajin-jiki-magayi nunki uku, tare da janye tallafin kudin cefanen wata-wata da kasar ke bai wa marasa galihu.

Saudiyya ta kara harajin-jiki-magayi (VAT), daga kashi 5% bisa 100% zuwa 15% bisa 100%. Kamar yadda Ministan Harkokin Kudade, Muhammad all Jadaan ya shaida a ranar Litinin.

Jadaan ya ce wannan al’amari ya faru ne saboda mummunan karyewar tattalin arzikin kasa, sakamakon karyewar farashin danyen man fetur a duniya.

Ya ce ya zama tilas a bijiro da wadannan hanyoyin tsuke bakin aljihun tattalin arzikin kasar tare da takaita kashe kudade a fannonin da ba su da muhimmanci ga gwamnatin kasar.

“Za a daina bayar da tallafin da ake bai wa marasa galihu a duk wata, tun daga ranar 1 Ga Yuni. Karin harajin-jiki-magayi kuwa zai fara aiki daga ranar 1 Ga Yuli, 2020.

Kamfanin Dillancin Labarai na Saudi Press Agency ya wallafa wannan bayani a shafin sa na intanet.

“Za mu kara harajin kuma mu janye bayar da tallafin domin mu samu karin kudaden shiga akalla Saudi Riyal biliyan 100. Wato kwatankwacin naira tiriliyan 10.3.

Cikin 2018 ne Gwamnatin Tarayya ta kirkiro harajin-jiki-magayi, wato ‘VAT’, domin samun kudi a rage dogaro da ribar man fetur. A gefe daya kuma sai ta yanka wa kowane marasa galihu alawus na rage fadadin tsadar rayuwa.

Masu lura da al’amurran kasar dai sun ce akwai yiwuwar jama’a su nuna rashin amincewa da wannan tsauraran matakan da Saudiyya ta dauka a na tsakiyar fama da annobar cutar Coronavirus.

Share.

game da Author