Muna nan muna ci gaba da yin bincike kan inganci ‘Hydroxychloroquine’ wajen warkar da Korona – NAFDAC

0

Awowi 24 bayan 24 bayan Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta sanar cewa za ta dakatar da gudanar da yin bincike don gano ingancin maganin ‘Hydroxychloroquine’ wajen warkar da cutar Covid-19, Hukumar kula da ingancin magunguna da abinci ta Najeriya NAFDAC ta ce za ta ci gaba da yin nata binciken kan maganin.

Shugaban Hukumar NAFDAC Mojisola Adeyeye ta sa Sanar da haka a tashar talabijin din TVC ranar a farkon wannan makon.

Mojisola ta ce duk da cewa kungiyar WHO ta dakatar da gudanar da bincike akan maganin NAFDAC za ta ci gaba da binciken.

Chloroquine magani ne da masana kimiyan magunguna suka hada shi tun a shekarar 1940 domin maganin zazzabi cikin sauro.

Sakamakon bincike ya nuna cewa maganin hydroxychloroquine na maganin Covid-19 a jikin mutumin da cutar ba ta yi masa illa ba.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa yana shan maganin chloroquine domin samun kariya daga kamuwa da cutar Covid-19.

Bayan haka gwamnan jihar Bauchi Mohammed Bala ya umurci ma’aikatar kiwon lafiya a jihar da su yi amfani da maganin chloroquine wajen kula da masu fama da cutar.

Ya ce chloroquine na daya daga cikin magungunan da ya sha ya samu lafiya a lokacin da ya kamu da cutar a kwanakin baya.

Sai dai kuma Shugaban kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar cutar COVID-19 kuma sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya gargadi mutane su daina amfani da maganin hydroxychloroquine domin warkar da cutar COVID-19.

Mustapha ya yi Wannan kira ne cewa har yanzu masana kimiyyar magunguna ba su tabbatar wa gwamnatin Najeriya ko maganin chloroquine na da ingancin gwarkar da cutar Covid-19 ba.

Share.

game da Author