ADAMAWA: Hannun mu ya kaiga damko naira biliyan 10 na UBEC mallakin jihar da aka barsu kwance a Asusun hukumar – Fintiri

0

Gaamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri ya bayyana wa mutanen jihar Adamawa cewa gwamnatin sa ta kaiga damko wasu kudade har naira biliyan 10 na inganta karatun firamare na bai daya dake jibge a asusun hukumar da gwamnatin baya ta yi biris da su.

Wadannan kudi dai na jibge a asusun hukumar ne tuntuni gwamnatin baya bata nemi ciro su tayi aiki da su ba musamman wajen inganta karatun firamare a jihar.

Fintiri ya ce ” Da muka dare gwamnati sai muka fara bibiyan ina wadannan kudade suke. Anan ne muka gano cewa ashe tun a 2015 gwamnatin jihar ba ta nemi karbar su ba. Amma mu mun samu damar damko su kuma za muyi aiki dasu na inganta karatun ‘ya’yan mu.

Bayan haka Fintiri ya ce gwamnatin sa ta biya wa ‘yan asalin jihar kudaden jarabawar kammala karatun Sakandare wato WAEC, NECO, NABEB da NBAIS, inda yace rabon da a yi haka a jihar tun shekarar 2007.

A karshe gwamna Fintiri ya ce, gwamnatin sa ta kara wa hukumomin tsaron jihar karfin guiwar tunkara mahara da suka addibi yankunan jihar da kuma kawo karshen ta’addanci ta hanyar siya wa hukumomin tsaron motocin aiki har 60.

Ya ce a dalilin haka manoma za su samu damar komawa gona domin noma amfani mai yawa.

Share.

game da Author