ZAMFARA: ‘Yan sanda sun kama masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba 251

0

Rundunar ‘Yan sanda jihar Zamfara ta damke masu wasu da ake zargi da hakar ma’adanai ba bisa ka’ida 251.

Kwamishinan ‘Yan sandan jihar Zamfara, Usman Nagogo ya bayyana haka a lokacin da yake faredin wadanda ake zargin a hedikwatar ‘yan sanda dake Gusau.

Bayan haka Nagogo ya tunsar da mutane wasu yan kasar Chana biyu da aka cafke a kwanakin baya da ke da hannu a hakar ma’adinan ba bisa ka’ida ba.

Kwamandan sojoji dake Birged ta 1, Bello Musliyu ya jagoranci zaratan jami’an tsaro zuwa wuraren da ake wannan kake-hake da suka hada da Kawaye, Zugu, Dan Kamfani, Bagega da kuma Dareta da Daki-Takwas a karamar hukumar Bukuyyum.

Baya ga wadanda aka kama, an kwace injinan ban ruwa 12, babura 25 da sinadarin wanke gwal da wasu tarkacen aiki.

A karshe ya gargadi mutane da su umarnin gwamnati su dakata daga aikin hako ma’adinai ba bisa ka’ida ba yana mai cewa duk wanda aka kama zai kuka da kan sa.

Share.

game da Author