Korona ta yi sanadiyyar rasuwar likita Nasir a Jigawa

0

Shugaban kungiyar likitocin Najeriya reshen jihar Jigawa, Nura Basirka, ya bayyana cewa kungiyar ta rasa wani mamban ta kuma likita a asibitin gwamnatin Tarayya dake birnin Kudu, jihar Jigawa.

Basirka ya ce marigayi Nasir mai shekaru 36 ya rasu ne bayan fama da yayi da sarkewar numfashi har Allah ya dauki ran sa. ” daga baya da aka dawo da sakamakon gwajin da aka yi masa sai yanuna yana dauke da Korona.

COVID-19: An sallami ma’aikatan kiwon lafiya 29 daga asibiti a jihar Jigawa

Shugaban Kungiyar likitocin Najeriya NMA reshen jihar Jigawa, Nura Basirka ya bayyana sallamar ma’aikatan kiwon lafiya 29 da suka kamu da cutar Covid-19 a jihar daga asibiti.

Basirka ya fadi haka wa PREMIUMTIMES a garin Dutse ranar Alhamis.

Ya ce wadannan ma’aikatan kiwon lafiya sun kamu da cutar ne yayin da suke kula da masu fama da cutar a asibitocin dake jihar.

“Likitoci 12 da nas-nas 17 na daga cikin wadanda aka sallama a jihar.

Rashin biyan ma’aikata alawus

Basirka ya ce har yanzu gwamnatin jihar na biyan ma’aikata da tsohon tsarin biyan alawus ne a jihar.

“Gwamnati ta yi wa ma’aikatan kiwon lafiya dake yaki da cutar Covid-19 alkawarin yin karin kudaden da take basu a matsayin alawus amma har yanzu gwamnati na biyansu Naira 5,000 kamar yadda yake ada.

Basirka ya jinjina samar wa ma’aikatan lafiya kayan samun kariya daga kamuwa da cutar da gwamnati ta yi yana mai cewa hakan da gwamnati ta yi zai taimaka wajen kare ma’aikatan daga kamuwa da cutar.

Idan ba a manta ba gwamnatin jihar ta bayyana cewa ta sallami wasu almajirai da aka dawo musu da su daga wasu jihohin a dalilin rashin samun su dauke da Korona.

Gwmanati ta ce mafi ywan wadanda aka gwada, zazzabi da ciwon ciki suke fama da, yara 28 ne kacal aka samu na dauke da cutar.

Share.

game da Author