Dan sanda ya bindige abokin aiki sa, ya bude wa wasu wuta

0

Wani dan sanda a jihar Legas ya bude wa abokanan aikin sa wuta inda nan take ya kashe mutum daya sauran kuma suka arce babu rauni a jikin su.

Kakakin rundunar ‘yan Sandan jihar Legas, Bala Elkana ya bayyana cewa dan sandan ya birkice ne bayan musu ya barke a tsakanin sa da abokan aikin sa. Daga nan sa ya juya kan bindiga ya bude musu wuta babu kakkautawa. Nan take dai ya kashe daya sauran kuma kowa zuba da gudu don cecen ran sa.

Sufeto Monday Gabriel ne ya aikata wannan ta’asa. Ya kashe Felix Okagbo da tuni har an jibge gawar sa a dakin ajiye gawarwaki, dake Asibiti a Legas.

Bayan ya aikata wannan mummunar aiki sai ya shiga motar yan’sanda ya fuzge ta yayi hanya babbar gadar Legas yana ta harbe sama domin a bashi wuri.

An yi sa, wasu yan sandan a bariga suka cafke shi. suka dawo dashi caji ofis.

Elkana ya ce an tafi da Monda asibiti domin a duba kwakwalwar sa ko ya tabu ne. Sannnan kuma ya kara da cewa za a gudanar da bincike mai zurfi domin gano me ya auku har wannan dan sanda ya bindige abokin aikin sa sannan ya nemi kashe sauran.

Share.

game da Author