Za ka yi ragaraga da Najeriya da irin salon mulkin ka na nuna bangaranci a nade-naden gwamnati – Dangiwa Umar ga Buhari

0

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna Dangiwa Umar ya ya gargadi shugaban kasa da kakkausar murya cewa yadda yake nuna son kai da fifiko a nade-naden sa zai iya jefa Najeriya cikin halin tashin hankali mai muni.

A wata budaddiyar wasika da ya rubuta wa shugaba Buhari, Dangiwa Umar ya bayyana cewa dama kuma Najeriya na cikin rudanin rabuwar kai a yanzu.

Dangiwa ya ce Buhari ya fi nuna sonkai da bangaranci a nade-naden shugabannin rundunonin tsaron kasar nan.

Bayan haka Dangiwa ya kawo misali da yadda gwamnatin Buhari ta ci mutuncin tsohon babban maisharia na kasa Walter Onnoghen wanda dan asalin jihar Cross Rivers ne wato yankin Kudu Maso Kudu. Duk da yana da damar Buhari ya amince da nadin shi ya ci gaba da zama a kujerar babban maishari na kasa Buhari ya san yadda yayi ya sauya shi da dan Arewa da karfin mulki.

Sannan kuma ya tunasar da shugaba Buhari kalaman da yayi a lokacin da yake rantsuwa cewa shi na kowa ne. ” Abin da yake yi ya saba da wannan kalamai nasa.” Inji Umar

” Duk da haka kuma ina so in tuna wa shugaban Kasa cewa nadin babban alkalin kotun daukaka kara na kasa na tafe, kuma ya sani cewa Alkali Monica Dongban Mensem, wanda ‘yar Arewa ce kuma kirista na nan tana rike da kujerar na wucin gadi a karo na biyu. Kuma alamu sun nuna cewa akwai yiwuwar ba ita bace Buhari zai nada.

” Idan ko ba ita bace za a nada wanda ke bi mata, musulmi ne dan Arewa. Idan har ya kai ga an wancakalar da ita an nada wani musulmi, hakan zai nuna cewa tabbas baka mutunta kamanka da kayi ba a baya na kai na kowa da kowa ne.

” Ni dai zan gaya maka gaskiya tsantsagwaranta, yadda kake nade-naden manyen ofisoshin gwamnati ta hanyar fifita ‘yan wani yankin kasar nan abin tashin hankali da zai iya kai kasar nan ya baro.

” Tabbas za a ce ka yi nasara a gwamnatin ka amma fa babbar nasarar ita ce zabe da kaci. A karon farko an samu wanda ya kada gwamnati maici a Najeriya. Hakan kuma ya yiwune saboda amincewa da talakawa suka yi cewa zaka maida musu da madaci Zuma.

” Kuma ina so ka sani cewa ba ayyukan da kayi bane kawai zai kwace ka idan ka kammala wa’adin mulkin ka. Har da yadda ka samar wa mutane tsaro, shugabanci da yadda aka rayu aka kasa a lokacin ka.

Dangiwa Umar ya hori shugaban Buhari da ya yi mulkin don kowa da kowa ba mulkin bangaranci ba.

Share.

game da Author