Tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Inginiya Mua’azu Magaji ya bayyana cewa sakamakon gwajin jinin sa da aka yi ya nuna shima ya kamu da cutar coronavirus.
” A Safiyar Alhamis ne hukumar NCDC ta gabatar da sakamakon gwajin cutar da aka yi mun kuma ya nuna ina dauke da ita. A yanzu dai an kai ni daya daga cikin asibitocin kula da wadanda suka kamu da cutar Kano.
Idan ba a manta ba a ranar 18 ga watan Afrilu ne Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya fatattaki kwamishinan Ayyukan jihar, Engr. Mu’azu Magaji daga kujerar kwamishina a jihar.
Ganduje ya yi haka ne saboda zargin wai kwamishinan yayi kalaman batanci da ga marigayi Abba Kyari a lokacin da ya samu sanarwan rasuwar sa.
Saidai kuma daga baya Magaji ya ce ba a fahimci abinda ya ke nufi bane a wancan lokaci. Hakan bai sa gwamna Ganduje ya dawo da shi ba.