Masu kiwon kaji a sassa daban-daban na kasar nan dangane ya asarar da suke yawan dibgawa sakamakon rashin cinikin da ba su samu saboda kakaba dokar hana walwala da aka yi a wasu jihohi.
Sun ce yanzu sun daina samun kasuwa saboda kulle mutane da aka yi a gida. Yanzu rashin cikini na kara gurgunta musu ciniki, kuma su na dibga asarar kwayaye da kajin da ake kyankyashewa.
Duk da gwamnatin tarayya ta sassauta doka a jihohin Lagos, Ogun da babban birnin tarayya Abuja, kuncin rayuwar da jama’ar suka shiga a lokacin zaman gida, ya sa an daina tururuwar sayen kwai.
Yanzu Cin Kaji Da Kwai Sai Wane Da Wane
Duk da dai daga baya an cire dokar zaman gida dole a kan masu abinci da wasu kayan abinci da masarufi na musamman, karancin kudi a hannun jama’a da kuma rashin walwala gami da kulle wurare duk ya sa an daina sayen kaji da kwayaye sosai.
Wani mai kiwon kaji a Abuja, mai suna Idris Olawaju, ya ce matsalar Coronavirus ta sa sun daina samun kwayaye sosai, babu ciniki, kuma kwayaye na lalacewa saboda rashin masu saye.
“Kafin fara Coronavirus na kan yi cinikin naira N500,000 a rana daya. Amma a yanzu harkar ta yi matukar lalacewa, saboda dalilai da yawa.”
Ya ce akwai matsalar zirga-zirga, sannan kuma makarantu duk suna kulle. “Idan makarantu su na bude an fi cinikin kwai sosai. Amma yanzu asara kawai su ke dibgawa.
“A baya mu kan bayar da sarin kires daya na kwai kan Naira N750 zuwa naira N800. Amma yanzu da babu kudi a hannun jama’a, sai su rika cirjewa su na cewa a saida musu kites daya naira N650 ko N700.
“To idan ba mu sayar musu ba, za su bar mu da kwan su lalace. Idan muka sayar a haka kuma, to ko abincin kaji ba za mu iya saya mu watsa wa kajin ba.”
Shugaban Kungiyar Masu Kiwon Kaji na Jihar Kaduna, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa, ai masu harkar kwai da kaji a Kaduna sun di na ko’ina ji a jikin su.
Ya ce harkar ta lalace, farashi ya yi rugu-rugu, kuma duk da haka babu masu saye. Saboda an kulle kowa a gida, babu zirga-zirga, yanzu ko ‘yan tsaki ma ba a saye.
“Yanzu ba ma ta sayen kwai ake yi ba. Kwai ya karye, kuma babu masu saye. Ka san Hi kwai ya na da lokaci. Idan ba a sayar da shi da wuri ba, lalacewa ko rubewa ya ke yi.
Shi ma Yohanna Moses daga jihar Nasarawa, ya ce lalacewar kasuwar ta kai a yanzu su masu kiwon kaji da kwai ke bin kananan ‘yan sari da ‘yan tireda su na kai musu har inda suke.