Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 276 da suka kamu da cutar Coronavirus a kasar nan ranar Talata.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Talata, sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum 161, Ribas-36, Edo-27, Kaduna-19, Nasarawa-10, Oyo-6, Kano-4, Delta-3, Ebonyi-3, Gombe-2, Ogun-1 Ondo-1, Borno-1, Abia-1, Bauchi-1.
Yanzu mutum 8344 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 2385 sun warke, 249 sun mutu.
Shugaban hukumar NCDC Chikwe Ihekweazu ya bayyana cewa akwai yiwuwar za a fara sallaman wadanda suka kamu da Korona da suka fara jin sauki daga asibitocin kasar nan.
Ihekweazu ya fadi haka ne a zaman da kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar cutar Covid-19 a Abuja.
Ya ce gwamnati na yunkurin daukan wannan mataki ne bisa ga sakamakon binciken da aka gabatar game da cutar dake nuna cewa za a iya sallaman wanda ke dauke da cutar daga asibiti idan ya fara jin sauki a jikinsa. Zai koma gida ya killace kan sa ma’aikata na zuwa suna duba shi suna bashi magani.
” Muna duba yiwuwar wannan abu har yanzu domin ganin ko za a yi aiki da shirin a kasar nan. Sannan muna wayar wa mutane kai game da haka saboda gujewa korafe-korafen da za su yi idan gwamnati ta amince a rika haka.
Karancin gadajen kwantar da marasa lafiya a kasar nan.
Bayanai sun nuna cewa gwamnati na yunkurin daukan wannan mataki ne saboda karancin gadajen kwantar da masu fama da cutar a kasar nan.
Bincike ya nuna cewa jihar Legas, Kano da Abuja na cikin wurarren dake fama da karancin gidaje a kasar nan kuma sune suka yawan masu dauke da cutar.
Ihekweazu ya ce gwamnati na yin nazarin yadda za a kima ana kula da mutane a gidajen su ne maimakon idan sun kamu a dauko subzuwa asibiti saboda karancin gadajen asibiti.
“A duk fadin kasar nan gadajen kwantar da masu fama da coronavirus guda 3,500 ne muke da su sannan a yanzu haka asibitocin killace masu fama da cutar na gab da cika a jihar Legas.
Yanzu mutum 7016 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 1907 sun warke, 211 sun mutu.
Yi wa mutanen da suka warke gwajin cutar sau daya a maimakon biyu.
Ihekweazu ya ce nan gaba za a fara yi wa wadanda suka warke gwajin cutar sau daya ne maimakon sau biyu da aka saba yi.