COVID-19: An gano mutum 27 da suka yi cudanya da Dan majalisar Nasarawa da ya rasu

0

Gwaman jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya bayyana cewa an gano mutum 27 da suka yi cudanya da dan majalisar dokokin jihar Suleiman Adamu wanda ya rasu sakamakon kamuwa da cutar Covid-19.

Sule fadi haka ranar Talata a zaman da ya yi da Jami’an tsoron jihar a Lafia.

Ya ce mutum 27 din da aka gano na daga cikin mutanen da Suleiman Adamu ya yi cudanya da su a karamar hukumar Nasarawa ne kawai.

Ya ce wadannan mutane sun hada da iyalansa da duk mutanen da suka je jana’izar sa.

Sule ya ce gwamnati za ta ci gaba da yin bincike domin gano sauran mutanen da mamacin ya yi cudanya da su baya ga ‘yan jihar Nasarawa.

Ya ce gwamnati ta bude asibitocin kula da mutanen da suka kamu da cutar a duk kananan hukumomin jihar.

An ranar Litini na wannan mako ne Gwamnatin Jihar Nasarawa ta bada sanarwa cewa an rufe majalisar jihar bayan daya daga cikin mambobin ta ya mutu sakamakon cutar Coronavirus.

An rufe majalisar domin a samu damar bin dukkan mambobin daya bayan daya da ma sauran wadanda suka yi mu’amala da mamacin a cikin kwanakin da suka gaba ta.

Kakakin Majalisa da sauran mambobi duk sun yarda su killace kan su, kuma an debi samfarin jinin su domin yin gwaji.

A yanzu dai mutum 12 ne suka kamu da cutar a jihar, mutum daya ya mutu.

Share.

game da Author