Kungiyar Likitoci NMA reshen jihar Kogi ta koka kan yadda gwamnatin jihar ta ki yi wa mutane gwajin cutar Covid-19 a jihar.
Shugaban Kungiyar Kabir Zubair ya bayyana cewa rashin yi wa mutane gwaji na iya jefa jihar cikin mummunar yanayi domin mutane da dama za su iya kamuwa da cutar ba tare da an gano ba wanda idan haka ya faru dakile yaduwar cutar zai yi wuya.
Zubair ya ce yi wa mutane gwajin domin gano wadanda suka kamu da cutar na daga cikin hanyoyin dakile yaduwar cutar.
A yanzu haka jihar Kogi da Cross Rivers ne jihohin da cutar Covid-19 bata bullo ba a Najeriya.
Daga watan Fabrairu da cutar ta bullo zuwa yanzu an yi wa mutum 19,512 gwajin cutar.
Hakan ya sa an gano mutum 2,948 dake dauke da cutar kuma 98 sun mutu a Najeriya.
Idan ba a manta ba a watan da ya gabata shugaban Hukumar NCDC Chikwe Ihekweazu ya koka da karancin yawan jinin mutane da jihohin Kogi, Nasarawa, Yobe da Cross River suka aiko domin a auna ko za a iya samun wadannan suka kamu da cutar.
Ihekweazu ya zargi wadannan jihohi da boye mutanen dake dauke da cuta domin a ganinsa ba za a rasa mutanen dake fama da cutar da ta yi kama da mura ko kuma nimoniya ba.
Gwamnati jihar Kogi ta maida martanin cewa har yanzu babu wanda ya kamu da cutar jihar.
Kwamishinan yada labaran jihar Kingsley Fanwo ya ce gwamnati na da masaniya game da yadda ake tilasta mata wajen yin gwajin cutar domin gabatar da mutanen da suka kamu.
Ya ce gwamnati na da labarin yadda wasu ke kokarin ganin mutane a jihar sun kamu da cutar.
Fanwo ya ce babu yadda za a yi gwamnati ta kirkiro mutanen dake dauke da cutar domin faranta wa wasu ma’aikatan kiwon lafiya rai bayan babu mu a jihar.
Discussion about this post