A daidai lokacin da Coronavirus ke ci gaba da ragargazar tattalin arzikin kasashen duniya, Gwamnatin Najeriya ta fara shirin gabzar naira tiriliyan 2 domin dumbuzawa cikin harkokin tattalin arzikin Najeriya.
Karamin Ministan Kudade, kasafin Kudi da Tsare-tsare, Clem Agba ne ya furta haka a Abuja, kamar yadda aka ruwaito.
Agba ya kara da cewa Gwamnatin Tarayya za ta ceto kamfanonin sufurin jirage, ganin yadda a kowane wata kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama ke yin asarar naira bilyan 21 a kowane wata, saboda Coronavirus.
Haka dai Agba ya fada a wurin wani taro a Abuja. Ya kara da cewa Gwamnatin a karkashin Kwamitin Bunkasa Tattalin Arzikin ya tsara wasu hanyoyi biyar da zai bijiro da ayyukan bunkasa tattalin arziki, inda za ta karkata kudaden su amfani al’umma.
“Wadannan kudade za su fito ne daga babban bankin Najeriya, CBN, Bankin Bunkasa Kasuwanci na Kasa da sauran alkawurran da Cibiyoyi da Hukumomin Duniya suka yi wa Najeriya na kudaden tallafi.
“Su kuma naira bilyan 2.5 da Bankin Duniya zai bayar lamuni, za ta gabji dala bilyan 1 a raba wa jihohi a matsayin lamuni.”
Agba ya ci gaba da bayyana yadda wasu tulin kudade za au shigo wa Najeriya da kuma yadda za su gangara har su isa gaban talaka ya ci moriyar su.
Annobar Coronavirus ta ragargaza tattalin arzikin Najeriya ta fannoni da dama.
Babbar hanyar da cutar ta yi wa tattalin arzikin kasar nan lahani, ita ce mummunar kariyar da farashin gangar danyenan fetur ya yi a duniya.
Najeriya ta yi kasafin kudin 2020 a kan a kan dala 57 a kowace ganga daya. Amma tilas ta sassauta kasafin zuwa dala 30.
Hakan ya tabbatar da cewa kusan kashi 45 bisa 100 na alkawurran da Buhari ya yi a kasafin 2020, ba za su tabbata ba.