Rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi ta bada sanarwar damke mutane 10 da ake zargi da hannu wajen lakada wa fasto duka da zabga masa bulala 35.
Bayan sun daure masa hannaye biyu ta baya, sun kuma tilasta shi yin wanka da ruwan kwata.
Kakakin Yada Labarai ta ‘yan sandan Ebonyi, Lobeth Odah, ta ce ‘yan sanda sun kama gogarman ‘yan jagaliya mai suna Julius Amadi da wasu yaran sa 9.
“Su ne su ka kama faston tare da wani Eze Ogbonna, su ka kai shi filin kwallon Ogo, su ka rika gallaza masa azaba.
Lamarin ya faru a garin Amasin, cikin Karamar Hukumar Afikpo.
An yi zargin sun lakada masa duka da tozarta shi saboda ya soki Shugaban Karamar Hukumar Afikpo ta Arewa, Ogbonnia Oko-Enyim a Facebook.
PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda aka rika zabga wa fasto bulala 35, an yi masa wanka da ruwan kwata don a ya soki Shugaban Karamar Hukuma a Facebook.
‘Yan jagaliya sun tirsasa wani fasto yin wanka a cikin kwata, bayan an zabga masa bulala har sau 35.
An yi wa faston wannan wulakanci ne bayan an zarge shi da sukar Shugaban Karamar Hukuma a Jihar Ebonyi.
Mai wa’azin, mai suna Chukwu Obeni, an ce ya rubuta labarin da ba gaskiya ba a shafin sa na ‘Facebook a kan Oko Enyim, Shugaban Karamar Hukumar Afikpo ta Arewa da ke Jihar Ebonyi.
Nuna wannan cin mutunci da aka yi wa mai wa’azin a been bidiyo da kuma hotunan, ya jawo jama’a da dama na yin tir da yadda ‘yan siyasa su ka maida kan su wasu Fir’aunonin da ba su jimirin a soki ra’ayin su.
Wani mai rajin kare hakkin jama’a mai suna Samson Nweke, ya ce shi da wasu ne suka dauki faston zuwa wani asibitin kudi, inda ya ke kwance a yanzu haka, ana duba lafiyar sa.
Bidiyon da aka nuna a twitter, an ga inda ake zabga masa bulalar doki har sau 35. Sannan kuma aka sa ya rika wanka da ruwan kwata, tsawon wasu ‘yan mintina.
Nweke ya ce za su bi wa faston hakkin sa daga wannan cin zarafi da aka yi masa.
Kakakin Yada Labarai ta ‘Yan Sandan Ebonyi, Loveth Odah, ta ce an kama mutum daya kuma ana bincike.
Ko cikin azumin nan a Jihar Kano wani Hakimi ya sa limami share kofar gidan sa, bayan an tsatstsala masa bulala, saboda karya dokar hana yin jam’i, don gudun kamuwa da Coronavirus.