Boko Haram sun yi wa garin Dapchi luguden wuta, sun banka wa gidaje wuta

0

Rahotanni sun tabbatar da cewa Boko Haram sun kai hari a garin Dapchi, da ke cikin Jihar Yobe, inda har gidaje su ka rika bi su na banka musu wuta.

Harin wanda aka kai misalin 7 na dare ranar Litinin, ya sa mazauna garin sun rika tserewa daga garin.

Wata majiya ta ce daga baya sojojin Najeriya sun kai ceto, inda kowane bangare ya ja daga aka rika barin wuta.

Har cikin dare an ci gaba da gumurzu tsakanin Boko Haram da sojojin Najeriya.

Dapchi dai can ne idan za a iya tunawa Boko Haram suka daliban sakandare 117 lokaci guda. Biyar suka mutu a hanya, daga baya an kulla yarjejeniya suka saki sauran, amma banda Leah Sharibu, wadda suka ki saki, saboda an ce ta fita daga addinin Kirista ta Musulunta, amma ta ki.

An kai wannan hari ne a ranar da wasu Boko Haram din suka kai hari a Baga, amma su ka kwashi kashin su a hannu daga barin wutar da sojojin Najeriya suka yi musu.

An kai wadannan hare biyu ne daidai lokacin da sojojin Najeriya ke ikirarin cewa sun kusa gamawa da Boko Haram, saura kiris.

Wasu rahotannin da suka rika fitowa daga bakin mahukuntan sojojin sun ce Shugaban Boko Haram Shekau ba neman sulhu da sojojin.

Share.

game da Author