Shugaban Hukumar Kula da ‘Yan Bautar Kasa (NYSC), Ibrahim Shu’aibu, ya bayyana cewa ba za su yi karambanin saurin gayyatar wadanda suka kammala digiri zuwa Sansanin Masu Bautar Kasa (NYSC), saboda annobar Coronavirus.
Burgediya-Janar Shu’aibu ya yi wannan furuci ne a cikin wata tattaunawa da aka yi da shi.
Ya ce ba za su yi gaggawa yanzu ko nan gaba ba, amma da zaran hukumomin da abin ya shafa su ka ga lokacin kiran masu bautar kasa din ya yi, to za a gayyace su kowa ya kai kan sa sansanin jihar da aka tura shi.
Ya tunatar cewa Rukunin B na 1 na zaune a sansani ne cutar ta barke a Najeriya, wanda hakan ya tilasta dole aka gaggauta sallamar kowa ya garzaya gida.
Sai ya ce idan kurar Coronavirus ta lafa, to su da ba su kammala karbar horon su ba ne za a fara kira su je su kammala kwanakin da suka rage musu karasawa.
“Ba mu san takamaimen ranar komawar su ba tukunna. Saboda ka san tsarin Sansanin NYSC kamar tsarin sojoji ne ko kuma sauran fannonin tsaro. Sai an ba mu umarni idan komai ya lafa sannan za a bude sansanonin NYSC din.”
Daga nan sai ya jinjina wa shirin koyar da NYSC sana’o’i a sansanoni, wanda ya ce an samu nasarar da har kudin shiga yaran suka rika samu.
“Mun ga yadda suka bazama wajen samar da takunkumin rufe fuska wanda suka rika dinkawa da kan su, sun samar da ruwan sabulun wanke hannu da sauran kaya ko sinadaran kare kai daga cutar Coronavirus.”
Ya ce a yanzu haka akwai masana’antar yin biredin NYSC da ruwan sha na roba a Kubwa, Abuja. Sannan ‘Yan NYSC da dama sun bazama kiwon kifi da na dodon-kodi.
Discussion about this post