Jami’o’i ne suka ribbaci gwamnati ta biya matattun malamai albashi -Akanta Janar

0

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa jami’o’i ne suka ribbaci gwamnati su ka tura mata sunayen matattun malaman da ba su duniya har aka biya su albashi.

Akanta Janar na Tarayya, Ahmed Idris ne ya bayyana haka, a matsayin maida martani ga Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa.

Idris ya ce ASUU ta na yi wa gwamnatin tarayya dariya wai ta biya matattu albashi, a kokarin kungiyar na tozarta tsarin biyan kudin albashi na gar-da-gar (IPPIS, wanda malaman jami’a suka dade su na nuna kin amincewa da shi.

“Lokacin da sa-toka-sa-katsi ta yi tsami da malaman jami’a, sai Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umarni a biya su albashin su. Sai mu ka tura wa Hukumar Kula da Jami’o’i sanarwa cewa, ta umarci shugabannin jami’o’i (VC) su aiko da sunayen malaman su.

“To tunda sun san ba wata daya kadai su ke bi albashi ba, maimakon su cire sunayen wadanda suka mutu da wadanda suka yi ritaya, sai suka hado da sunayen su duka, don su samu kudin aringizo.”

Ya wasu malamai har 1,180 ba su samu albashin su ba, saboda sunayen da Jami’o’i suka aiko na malaman sun sha bamban da sunayen su da ke cikin tsarin IPPIS.

“Sunayen su da aka tura ofishin IPPIS daidai su ke da wadanda jami’o’in da suke turawa su ka aiko mana ba. Wasu mata a cikin su sun yi aure, sun canja sunan uba zuwa sunan miji ba tare da sanar da ofishin IPPIS ba.”

Da ya ke karin haske kan wadanda aka zabtare wa kudade, Idris ya ce hakan ya faru ne saboda a baya ba a cire kudaden haraji da na Adashin Kudin Sayen Gidajen Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya.

Share.

game da Author