An sallami jaririya ‘yar wata hudu da ta kamu da Korona a Kaduna

0

Kwamishinan Lafiya ta jihar Kaduna Amina Baloni ta bayyana cewa an sallami jaririya da ta kamu da Korona a Kaduna.

Idan ba a manta ba, ita wannan jaririya ta kamu da Korona ne bayan an gano mahaifinta na yin zirga-zirga zuwa Kano.

Bayan haka kwamishina Baloni ta yi Karin haske game da matsayar Kaduna a aikin dakile yaduwar annobar Korona Bairos.

” Zuwa yanzu cutar Korona ta yadu zuwa mazabu 33 a kananan hukumomi 9 dake fadin jihar. Sannan kuma bayan gargadi da gwamnati ke yi na hana tafiye-tafiye zuwa wasu jihohi, Jami’an lafiya sun fantsama domin gano Wanda ya San wanda yayi mua’mula da Wanda aya kamu da cutar tun daga cikin garin Kaduna zuwa kauyukan jihar.

” Cikin mutum 232 da suka kamu a Kaduna,an sallami mutum 149, 7 sun mutu. Sannan kuma akwai yiwuwar kara samun wadanda suka kamu da cutar a jihar idan sakamakon gwajin sama da mutum 2000 da jihar tayi ya fito da kuma wanda za ta ci gaba da yi nan gaba.

Bayan haka, kwamishina Baloni ta kara da yin albishir cewa motar yin gwajin cutar da zai riga bi lungu-lungu, kwararo-kwararo domin yi wa mutane gwajin cutar a ko-ina ya iso jihar.

Sannan kuma wasu injinan yin gwajin 12 duk sun iso jihar. Za a saka su a duka asibitocin jihar domin yin gwajin cutar.

Share.

game da Author