KORONA: Najeriya ta samu karin mutum sama da 500 da suka kamu a ranar Asabar

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 553 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Asabar.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Asabar, sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum 378, FCT-52, Delta-23
Edo-22, Ribas-14, Ogun-13, Kaduna-12 Kano-9, Borno-7, Katsina-6, Jigawa-5
Oyo-5, Yobe-3, Plateau-3, Osun-1.

Yanzu mutum 9855 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 2,856 sun warke, 273 sun mutu.

Duk da yawan mutane da ake samu sun kamu da cutar a kullum a Najeriya, wasu da dama na ganin har yanzu ba a yi wa mutane gwajin cutar yadda ya kamata a kasar.

Jihar Legas na ci gaba da samun daruruwan mutanen da suka kamu da cutar Korona babu kakkautawa.

A ranar Asabar kawai, jihar Legas ta samu karin mutum sama da sama da 300. Akalla jihohi 12 sun samu karin mutane da suka kamu da kwayoyin cutar.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 4,755 cases, sai Kano – 951, FCT – 616, Katsina – 364, Edo – 284, Oyo – 280, Borno – 271,Jigawa – 270, Ogun – 259, Kaduna – 244, Bauchi – 236, Rivers – 204, Gombe – 156, Sokoto – 116, Plateau – 104, Kwara – 87, Delta – 80, Zamfara – 76, Nasarawa – 62, Yobe – 52, Akwa Ibom – 45, Osun – 45, Ebonyi – 40, Adamawa – 38, Imo – 34, Kebbi – 33, Niger – 30, Ondo – 25, Ekiti – 20, Enugu – 18, Taraba – 18, Bayelsa – 12, Anambra – 11, Abia – 10, Benue – 7 and Kogi – 2.

Share.

game da Author