Mahara sun sace attajiri dake kwance yana jinya, sun bukace naira miliyan 40 kudin fansa

0

Mahara dauke da manyan bindigogi sun sace wani attajiri mai suna Yusuf Maifata, kwance a gidansa yana jinya ranar Juma’a.

Maharan sun diran wa kauyen Sankara, dake karamar Hukumar Ringim, jihar Jigawa da dare da misalin karfe biyun saura na dare.

Sun yi ta harbin bindiga domin tsorata mazauna garin har suka samu suka afka gidan dattijon dake da shekaru 75.

Bayanai sun nuna cewa Koda maharan suka kutsa dakin Maifata sun same shi ranga-ranga a sume ne kwance a gadon jinya.

Daga baya an ce maharan sun Kira ‘yan uwan Maifata inda suka bukaci a biya su naira miliyan 40 kudin fansa sannan kuma su gaya musu wasu irin magunguna take Sha da kalan abincin da ake bashi.

Kakakin rundunar’Yan sandan jihar Jigawa Audu Jinjiri ya tabbatar da aukuwar wannab al’amari yana mai tabbatar wa mutane cewa ‘yan sanda zasu ceto dattijon da aka yi garkuwa da nan ba da dadewa ba.

Share.

game da Author