An damke sufeton dan sandan da ya bindige malami kan titi

0

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Lagos ta ce ta cafke Sufeto Charles Okoro, wanda ya bindige wani matashin malami, Fatai Oladipupo, a Lagos.

Sufeto Charles ya bindige Malam Fatai a unguwar Obabiyi, kan titi Igando cikin Lagos, a ranar Laraba.

Kakakin ‘Yan Sandan Lagos, Bala Wlkana, ya ce Sufeto Okoro ya na aiki ne a Ofishin Shiyyar Ikokun, Lagos.

Ya ce an kama shi tun a ranar Laraba din da ya aikata danyen aikin. Kuma ana binciken sa a hedikwatar ‘yan sandan Lagos.

Ya ce idan aka same shi da laifi, za a damka shi ofishin CID, wadanda za su bincike shi, sannan su gurfanar da shi a kotu.

Kwamishiman ‘Yan Sandan Jihar Lagos, Hakeem Odumosu, ya kai ziyarar ta’aziyya ga ‘yan uwa da abokan arzikin Fatai, kuma ya ce idan aka gama gudanar da bincike, aka samu wanda ake zargi da laifi, to za a hukunta shi kamar yadda doka ta tanada.

A kullum ana samun rahotannin yadda ‘yan sanda ke karbar toshiyar baki, gallaza wa jama’a, ko kuma bindige su dungurugum su rasa rayukan su.

Irin wannan gallazawar ce ta sa Kungiyar Likitocin Jihar Lagos yayin yajin aiki a ranar Talata, bisa yadda ‘yan sanda ke tozarta su a yanzu sin nan, lokacin Coronavirus.

Said dai kuma an sasanta da suka washegari ranar Laraba sun koma aiki.

Share.

game da Author