Gwamnatin Tarayya ta roki Gwamnonin da ke dage dokar hana walwala saboda Coronavirus, su canja tunani, domin hakan kan iya sake barkewar cutar fiye da kima a cikin al’umma.
Sakataren Gwamnatin Tarayya, kuma Shugaban Kwamitin Dakile Coronavirus na Shugaban Kasa, Boss Mustapha ne ya bayyana haka ranar Alhamis da dare, lokacin sa ya ke wa manema labarai bayani dangane da ci gaban da ake samu wajen yaki da cutar Coronavirus a kasar nan.
Duk da karin yawan masu cutar Coronavirus da ake samu a kasar nan, wasu jihohi sun tari-aradun cire dokar hana walwala suka bar jama’a ci gaba da harkokin su.
Daga cikin jihohin da suka dage dokar akwai Bauchi, Kano, Adamawa, Cross River, Barno, Ebonyi da sauran su.
Jihohin sun kyale jama’a cikin kasuwa, zuwa sallojin Juma’a da coci-coci.
Mustapha ya ce akwai barazana ga jihohin da aka bude yanzu ana al’amurra, duk kuwa da cewa cutar na kara yaduwa a yanzu a nan Najeriya.
Ya ce ya kamata a guji duk wani taro da ya kai nai akalla mutum 20 abin da ya yi sama.
“Su kan su yawan haduwar tsirarun mutanen 20 abin da ya yi sama kan iya zama barazana ta yadda za su iya kamuwa da cutar.
Ya na kunnen gwamnoni kuma ya roki su kara wayar da mutanen karkara kai dangane da cutar.
Idan ba manta ba, Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ce idan ba a yi da gaske ba, to akalla mutum milyan 250 za su iya kamuwa a Afrika.
Discussion about this post