Sai gwamnoni sun bada hadin kai za mu iya dakile Coronavirus – Lai Mohammed

0

Ministan Yada Labarai kuma mamba na Kwamitin Shugaban Kasa Mai Yaki Da Coronavirus, Lai Mohammed, ya ja hankalin gwamnonin Najeriya su bai wa Gwamantin Tarayya hakin kai domin kokarin dakile cutar Coronavirus a kasar nan.

Da ya ke tattaunawa ranar Juma’a a gidan talbijin da safe, Lai ya ce abin da wasu gwamnoni ke yi tamkar siyasa ce su ke yi da cutar Coronavirus a kasar nan.

Ya ce matsawar wasu gwamnoni ba su daina sa siyasa a lamarin ba, to ba za a iya samun nasarar korar cutar dungurugum ba.

Da ya ke amsa tambaya kan helikwafta da Gwamnatin Jihar Rivers ta kama kuma ta sa kotu ta kulle direbobin su biyu a kurkuku, Lai ya ce bai kamata abin ya kai ga haka ba, domin Gwamnatin Tarayya da ta sa dokar hana zirga-zirga ta ce banda masu ayyuka na musamman.

Ya ce tunda helikwaftan ya na yi wa gwamnatin tarayya aikin musamman ne, bai ma kamata jihar Rivers ta damke jirgin ba.

“Ya kamata kowa ya fahimci cewa gwamnatin tarayya na da ikon yin doka ko wani umarni akn kowane dan kasa, ko ma a wace jiha ya ke zaune ko aka haife shi.

Da ya juya kan tambayar sa da aka yi kan wasu gwamnoni da suka sassauta dikar hana zirga-zirga, Lai ya ce shirin korar Coronavirus ba zai yi wani tasiri ba sai gwamnoni sun bada hadin kai sosai

“Har yau cutar Coronavirus ba ta da magani. Shi ya sa aka kulle Legas, Abuja da kuma Ogun, inda ta fi yi wa illa. Saboda idan aka kwana 14, cutar za ta fito a jikin wanda ta kama.

“Duk wanda ta kama ba bu magani. To wata matsala ita ce mutanen da ba su killace kan su ba, za su iya ci gaba da baza cutar a cikin al’umma.

Gwamnonin da suka karya umarnin Gwamnatin Tarayya sun hada da Nysom Wike na Ribas, Bello Masari na Katsina, Akeredolu na Ondo, sai na Bayelsa da wasu daban.

Share.

game da Author