Gwamnan jihar, Katsina Aminu Masari ya sanar da garkame garin Daura, ba shiga ba fita a dalilin bayyanar coronavirus.
Gwamna Masari ya ce daga karfe 7 na safiyar Asabar, ba shiga ba fita garin Daura kuma kowa ya yi zaman dole a gida.
Hakan ya biyo bayan bayyanar cutar coronavirus har mutum Uku a garin.
Masari ya ce iyalan likitan da ya rasu kwanakin baya ne suka kamu da cutar.
” Mun aika da samfirin domin a yi gwajin cutar. Gwajin jinin mutum 23 aka dawo mana da shi, 20 ba su da shi, 3 sun kamu.
Gwamnan ya umarci mutane su loda abinci a gdajen su daga yau zuwa safiyar gobe Asabar domin zaman gida dole da za suyi a wannan lokaci.
Idan ba a manta ba gwamnatin jihar ta sassauta dokar hana walwala a jihar inda ta amince wa wuraren su rika zuwa salloli da taron coci-coci, sai dai ka da a rika dadewa.