Jami’an tsaro na sibul difens (NSCDC) sun damke wasu limamai biyu a jihar Kwara da suka karya dokar jihar na hana taro da ya hada da salloli a masallatai.
Jami’an tsaron sun kama wadannan limamai da karfe 1 na ranar Juma’a bayan sun Kammala sallah a masallatan su dake hanyar Adeleke a karamar hukumar Offa.
Jami’an tsaron sun garzayo wannan masallaci a daidai ana sallah sai ko mamu da ladan suka arce suka bai liman shi kadai tilo a tsaye ya kira’a.
Gwamnati ta kama limaman ne a dalilin karya dokar hana tarurrukan mutane sama da mutum 10 da gwamnati ta kafa domin dakile yaduwar coronavirus a jihar.
Wannan doka da gwamnatin ta kafa ya shafi yada da tarion mutane a kasuwanni musamman wadannan ba a siyar da kayan abinci suke yi ba.
Domin samun kariya daga kamuwa da cutar mataimakin gwamnan jihar kuma shugaban kwamitin dakile coronavirus a jihar Kayode Alabi ya sa a yi feshin magani a kasuwanni da sauran wuraren da mutane suka fi taruwa a jihar.
A makon da ya gabatar Jami’ar tsoro sun kama limamin masallacin Agege dake jihar Legas da dalilin karba dokar gwamnati.
Kuma gwamnati a jihar Kaduna ta kama wasu limamai biyu da suka karya dokar zaman gida suka gudanar da sallar juma’a.
A yanzu dai mutane 190 suka kamu da cutar, 20 sun warke sannan biyu sun mutu a Najeriya.
Lagos- 98
FCT – 38
Osun – 20
Oyo – 8
Akwa Ibom – 5
Ogun – 4
Edo- 4
Kaduna – 4
Bauchi – 3
Enugu – 2
and Ekiti – 2
Rivers – 1
Benue -1
Discussion about this post