Hukumar hana yadawar ctuttuka ta kasa (NCDC) ta bayyana cewa adadin yawan mutanen da zazzabin lassa ta kashe a kasar nan ya haura daga 176 zuwa 185.
NCDC ta ce an samu wannan karuwa ne a jihohin Edo, Ondo, Ebonyi, Bauchi, Taraba, Filato, Kogi da Delta sannan a cikin mako daya.
Duk da haka hukumar ta ce yaduwar cutar ta ragu a kasar sannan haka na da nassaba ne da ruwan saman da aka fara a wasu bangarorin kasan.
Bayan haka hukumar ta ce ta na kokarin ganin ta bude asibitocin kula da wadanda suka kamu da cutar a ko wani jiha a kasar nan.
A makon da ya gabata ne hukumar ta sanar cewa mutane 176 sun mutu a dalilin kamuwa da zazzabin lassa a kasar nan.
NCDC ta ce daga watan Janairu zuwa 22 ga watan Maris 2020 hukumar tayi gwajin jinin mutum 4012 inda sakamakon gwajin ya nuna cewa mutane 932 na dauke da cutar, 176 sun mutu.
ALAMUN KAMUWA DA ZAZZABIN LASSA
Ciwon kai: Yawaita fama da ciwon kai alama ne cewa lallai sai an duba mutum a asibiti, domin idan zazzabin lassa ta kama mutum ciwon kai na daga cikin alamun dake fara nunawa.
Zazzabi: Za a rika jin jiki yayi nauyi kamar zazzabi-zazzabi haka idan Lassa ta shiga jikin mutum. Zazzzabi ko masassara zai rika damun mutum a wannan lokaci.
Ciwon jiki: Jikin mutum zai rika yawan yi masa ciwo matuka. Ko ina zai rika jin ciwo yake masa. Hakan ma alama ce dake nuna an kamu da Lassa. Hakna kuma sun hada da ciwon gabobin, ciwon baya, yawan gajiya sannan a wasu lokutan har da ciwon kafafu.
Amai: Saboda zafin zazzabi da ciwon kai mutum kuma zai rika yawan yin amai.
Rashin iya cin abinci: Zazzabin lassa na hana mutum iya cin abinci. zaka ci gaba daya baka bukatan cin wani abu duk ko da cewa zaka rika jin yunwa.
Yawan yin Bahaya: Za a yi fama da yawan shiga bandaki a dalilin kamuwa da wannan cuta sannan hakan zai sa mutum yawan jin kishin ruwa.
Yawaita Suma: Idan har mutum ya kamu da wannan cuta, za a rika yawan suma saboda rashin lafiyar dake jikin mutum.
Jini: Za a rika zubar da jini ta wasu kafafen jiki musamman idan abin ya fara nisa ba a duba mutum a asibiti. Hakan na nuni cewa cutar ta fara yi wa mutum mummunar illa.
YADDA ZA A GUJEWA KAMUWA DA ZAZZABIN LASSA
1. Tsaftace Muhalli: A rika tsaftace muhalli a ko da yaushe. A kau da datti a kowani lokaci sannan a rika goggoge wuarare.
2. Zubar da Shara: Idan aka tara datti, kada arika barin su kusa da gida. A kai su can wajen da ake zubdawa a nesa ko kuma a rika konawa.
3. Killace Abinci: Yin haka zai taimaka wajen hana bera ko kwari shiga cikin abincin.
4. Dafa Nama: Kafin a dafa nama kamata a rika wanke shi da ruwan gishiri domin kashe duk wasu kwayoyin cuta dake jikin naman. A tabbatar naman ya dahu sosai kafin a ci.
Namun Daji: A nesanta kai daga yin mu’amula da namun daji musamman jinsin berayaye da birai.
5. Cin ‘ya’yan itatuwa: Kafin a ci ‘ya’yan itatuwa ko kuma ganye a rika wanke su sosai. Hakan na kau da datti a jikin su.
6. A daina barin dabbobin gida na shiga inda ake aje abinci: Kaji da wasu dabbobin da ake kiwon su a gida kan yi mu’amula da beraye a lokutta da yawa.
7. Toshe kafafen da suka bude: A tabbatar an toshe ramin da bera zai iya shiga cikin dakunan mu.
8. Tsafta: A yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu kafin da bayan an ci abinci sannan idan an kammala amfani da ban daki.
9. Ma’aikatan kiwon lafiya su tabbata sun nemi magani da zarar allurar da suka yi amfani da shi a jikin wanda ke dauke da cutar ya soke su.
10. Kona daji: Kona daji na daga cikin hanyoyin dake koro beraye zuwa cikin gidajen mutane. A rika kiyayewa wajen kona dazukan dake kewaye da mu. Mai makon haka a rika feshin magani.
11. Wanke gawa a cikin Daki: Shima hakan na da illa matuka. Maimakon a rika wanke gawa a cikin gida a rika yin sa a waje ne ko kuma inda ya kamata.
HANYOYIN SAMUN MAGANI
1. Da zarar mutum ya kamu da zazzabi a tuntubi likita domin tabbatar da cutar da mutum ke dauke da shi.
2 – Ba a iya kamuwa da cutar zazzabin Lassa idan an taba wanda ke dauke da cutar amma za a iya kamuwa da shi idan yawu, jini ko kuma zufan wanda ke dauke da cutar ya taba wanda ba ya da shi.
3 – Za a iya warkewa daga zazzabin lassa idan an gaggauta zuwa asibiti.
Discussion about this post