Hukumar hana yaduwar cututtuka na kasa (NCDC) ta sanar cewa mutane biyu sun kara mutuwa a dalilin kamuwa da cutar coronavirus a Najeriya.
NCDC ta ce daya ya mutu a jihar Legas sannan daya a jihar Edo.
A takaice dai adadin yawan mutanen da suka mutu a kasar nan sun kai 4.
Bayan haka hukumar ta kuma sanar cewa wasu mutane 20 sun kara kamuwa da cutar a kasar nan.
An gano 11 a jihar Legas, 3 a Abuja, 3 a Edo, 2 a Osun sannan daya a Ondo.
A yanzu dai mutane 210 ne ke dauke da cutar a kasar nan.
Daga ciki 25 sun warke 4 sun mutu.
FCT – 41
Osun -22
Oyo – 8
Akwa Ibom – 5
Ogun – 4
Edo- 7
Kaduna – 4
Bauchi – 3
Enugu – 2
Ekiti – 2
Ondo – 1
Rivers – 1
Benue – 1
Shugaban Hukumar NCDC Chikwe Ihekweazu ya ce gwamnati za ta hada hannu da bangaren masu zaman kansu domin kara yawan wuraren gwajin cutar.
A yanzu dai mutane 4000 ne ake yi wa gwajin cutar a rana a wuraren gwajin cutar a Najeriya.