Iyaye da ‘yan uwan wani matashi da ya dawo daga jihar Legas sun arce sun bar masa gida bayan ya dawo daga Legas a Unguwar Kurmi, karamar hukumar Igabi, jihar Kaduna.
Shi dai wannan matafiya, ya fara amai, da zazzabi mai zafi ne bayan dawowa daga Ikko, ganin haka kuwa sai ‘yan uwansa suka tattara nasu-ina su suka arce suka bar masa gidan.
Mai anguwan Kurmi Liman Hamisu, ya shaida wa manema labarai cewa daga baya sai mutanen gari suka fada cikin fargaba ganin yadda yan uwan wannan matashi suka kauce daga gidan, tsoron coronavirus.
Liman ya ce daga nan ne suka gayyaci ma’aikatan kiwon lafiya na wannan karamar hukumar domin su duba wannan matashi da yake kwance.
Sannan aka kira ma’aikatan hukumar NCDC, domin su yi masa gwaji a tabbatar ko me ke tattare dashi.
” Da suka isa aka duba shi sai aka gano cewa zazzabi ne kawai ta kwantar dashi bayan ya dawo ba coronavirus ba.
Ya fara samun sauki sai dai har yanzu ‘yan uwan ba su dawo gareshi ba.
Wani jami’in kiwon lafiya na yankin ya taya matashin yin kira da rokon yan uwan sa da su dawo ga dan uwan su, cewa ba shi dauke da Coronavirus.
Jihar Legas ce ke kan gaba wajen yawan wadanda suka kamu da wannan cuta a kasar nan.
Akwai mutum sama da 100 sake kwance a Legas da suka kamu da wannan cuta.
Discussion about this post