SHIGA SHARO BA SHANU: Me ya hada hukumar jihar Kano da shirin ‘Kwana Casa’in’ na tashar Arewa 24 dake Satilite

0

Shugaban hukumar tace fna-finai na jihar Kano, Ismail Afakallahu, ya bayyana cewa wasu manyan shirye-shirye da ake nuna wa a gidan talabijin din Arewa 24 ba cika sharuddan hukumar tace fina-finai na jihar Kano ba.

Wadannan fina-finai kuwa sune (Kwana Casa’in da Gidan Badamasi).

Wadannan wasannin kwaikwayo sun shahara matuka a yankin Arewa domin kusan kowa musamman mata a gida da matasa suna kallon wadannan shirye-shirye.

Sai dai kash, hukumar tace fina finai ta jihar Kano karkashin Afakallahu, ta ce ba ana nuna wasu abubuwa a shirin da ya saba wa al’adun mutanen Arewa.

Sannan kuma ya saba wa dokar shirya wasan kwaikwayo na jihar Kano.

Afakallahu ya ce bayan haka ba a mika wadannan shirye-shirye ga hukumar tace fina-finai na jihar Kano ba kafin a rika saka wa.

Wadannan wasanni biyu sun shahara matuka da wasu ke ganin babu wasu tambadewa da ake yi aciki da har zai sa ace wai an dakatar da shirye-shiryen.

” Baya ga haka, shin Kano ce dole zata ba mutum damar shirya fim a Arewa ko kuma hukuma ta Kasa wato NBC. Shi wannan shiri a Satilite ake nuna shi, tashar ma ba ta jihar Kano ba ce sannan duk kasa ake kallo. Idan Baku so a Kano, sai ku toshe tashar a can. Yaya za ace kawai sai wata hukuma a Kano ce zata ce a dakatar.” Inji wani mazaunin Zariya, Jihar Kaduna.

” Ko a talabijin akan ce idan shiri bai yi maka ba, sai ka canja wani tashan, amma wannan wasan kwaikwayo ne, babu abinda ya bata shi, idan ku bai yi muku a Kano ba sai ku dai na haska tashar a Kano, ku bari wa wadanda su yayi musu. Ina kira ga Area 24, Kada su saurare su, domin ba tashar Kano bane.” Inji Hawwa Jawwa, daga Bauchi.

Share.

game da Author