Duk matafiyin da ya ratso ta Kaduna za a killace shi na kwana 14, ko kuma ya koma inda ya fito

0

Gwamnatin Kaduna ta sanar cewa daga ranar Alhamis, 9 ga watan Afrilu, duk wani matafiyi a akasa ko a mota da ya gitto ta iyakar Kaduna, za a kama shi a ajiye a wajen killace masu fama da coronavirus na kwana 14.

Wannan sanarwa ta fito daga ofishin kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna.

Kwamishina Samuel Aruwan ya bayyana cewa gwamnati ta saka dokar hana walwala a jihar Kaduna da kuma ratsawa ta jihar domin zuwa wata jiha. Saboda haka duk wani matafi da yake da burin yin tafiya kuma sai ya biyo ta Kaduna, ya canja shawara domin ko ya yi shirin zaman kwanaki 14 a killace ko kuma a maida shi inda ya fito. In ji Sanarwan

Sai dai kuma sanarwar ta ce akwai wadanda za a bari su rika wucewa idan suna da muhimmin uzuri na tafiya ko ratsawa ta jihar.

Manyan hanyoyin da aka hana bi ko ratsawa sun hada da Titin Kaduna-Abuja, Kaduna-Birnin Gwari, Kaduna-Zaria-Kano, Titin Kachia, Titin Bwari-Jere-Kagarko, Titin Gumel-Kwoi-Keffi, Titin Zaria-Funtua da Titin Jos-Manchock.

Sanarwar ta ce ba wadannan tituna da aka lissafo a baya ba, har da wasu da ba a fade su ba.

Jihar Kaduna na da akalla mutum 5 da suka kamu da cutar coronavirus a kasar nan, ciki har da gwamnan jihar Nasir El-Rufai.

Zuwa yanzu akwai akalla mutum 254 da suka kamu a Najeriya, 6 sun mutu.

Share.

game da Author