Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana sanar da kara kwanaki 30 daga ranar Litini na ‘Zaman Gida Dole’ da hana walwala a jihar Kaduna.
Sanarwar haka ta fita daga bakin Kakaikn gwamnatin jihar Muyiwa Adekeye wadda shine ya saka wa takardar hannu a madadin gwamna el-Rufai.
” Ganin yadda ake ta samun karuwar yawan wadanda suka kamu da cutar a musamman babban Birnin Tarayya, Abuja, sannan kuma da tabbaci da aka samu cewa tafiye-tafiye a tsakanin jihohin dake zagaye da jihar na yada cutar, kwamitin ta bada shawarar a tsaurara matakai don kare mutanen jihar.
” Gwamna El-Rufai ya amince bayan an duba rahotan yadda dokar garkame mutane ya gudana a Kaduna, daga wannan mako sau daya za a rika fita zuwa kasuwanni da dan walwala. Am bada ranar Laraba a matsayin wannan rana, gwamnati ta soke ranar Talata.
” Daga yanzu ranar Laraba ne kawai za arika fita, har sai an samu sahihan bayanai na an iya kakkabe wannan cuta.
” Sannan kuma duk wanda zai fita daga gidan sa daga yanzu sai ya saka takunkumin fuska dole kuma ayi nesa-nesa da juna a kasuwanni da zaman cikin mota. Gwamnati za ta wadata gajiyayyu, da wadanda basu da halin siya da takunkumin fuska. Bayan haka an yi kira ga mutane su garzaya ga tailoli su dinka musu takunkumin da za su iya wanke wa idan yayi datti.
” Dole a saka takunkumin fuska a fadin jihar, domin kare kai daga kamuwa da cutar.
1 – Dole kowa ya zauna a gida dole
2 – Ba a yarda a bude ofisoshi ba, Kasuwanni, wuraren shakatawa, shaguna, masallatai da coci-coci, wato wuraren bauta.
Wadanda aka yardarwa su ci gaba da zirga-zirga sune ma’aikatan kiwon lafiya, ma’aikatan Kashe gobara, ma’aikatan albarkatun ruwa da wutan lantarki sannan kuma da jami’an tsaro. haka kuma tankoki dake kai mai gidajen saida mai.
Wuraren saida abinci da kayan asibiti za a samar musu da tsaro.
Makarantu, wuraren ibada, wuraren shakatawa, filayen motsa jiki, gidajen giya, duk zasu ci gaba da zama a kulle.
Gwamnati ta hori mutane su cigaba da zaman gida, sannan su rika nesa-nesa da juna kuma a gujewa shiga taro ko cunkoso, a saka takunkumin fuska sannan a rika wanke hannu da ruwa da sabulu.
” Duk matafiyin da ya shigo Kaduna da gangar, za a killace shi na kwanaki 14, ko kuma ya koma inda ya fito. Sannan kada ya dauka za a killace shi don nishadi ne.
” Duk motar da aka kama shikenan mai ita zai rasa ta har abada domin zai koma mallakin gwamnati. Sannan duk kamfanin dake da mallakin wannan mota zai fuskanci hukunci. Domin za a kai shi kotu sannan za a kwace lasisin yin aiki a jihar Kaduna. Shima direban wannan mota sai ya biya tara ko a daure shi. Haka kuma an dakatar da ayyukan Keke Napep, Acaba, Tasi da sauran su. duk wanda aka kama za a kwace abin hawan na dindindin, zai zama na gwamnati.
” An kirkiro Kotun tafi da gidan ka da za ta rike yanke hukunci nan take. Nan take za ka biya tara, in dauri ne ma duk anan za a yanke maka hukunci sannan kuma ma idan kwace abin hawanne ma duk anan ne za a kwace.
” Haka kuma motocin daukar mai, abinci, taki da kayan gona, kayan asibiti duk ban da su, sai dai suma din kada su wuce mutum uku a ciki.
” Duk wanda ya yi wa gwamnati sojan gona, wajen yi kamar shima mai jigilar kayan abinci ne, za a tuhume shi sannan a kwace masa matar ta zama na gwamnati.
Bayan haka gwamnati ta ce ta umarci duka shugabannin kananan hukumomin jihar su tabbatar wannan doka ya tabbata a Kananan hukumomin su.
” Gwamnatin Kaduna ta umarci duka manyan ma’aikatan ta, da ya hada da kwamishinoni, Manyan Sakatarori, masu ba gwamna Shawara, shugabannin ma’aikatu su ba da gudunmawar naira 500,000 a wannan watan Afrilu. Sannan za su rika bada rabin Albashin su duk wata har sai an bude gari.
Ma’aikatan gwamnati dake karbar albashin naira 67,000 duk wata za su rika bada kashi 25% na albasin su duk wata har sai an bude gari. Babu wani ma’aikaci da zai rasa kasa da naira 50,000, da zai rika maneji har zuwa a bude gari.
Bayan haka ya ce gwamnatin jihar zata yaba wa duk wanda ya taimakawa jihar da kudi, kaya, abinci, magani da sauran su. sannan kuma za a bayyana irin taimakon da ya bada baya ga takardar yabo da za a bashi.