COVID-19: Mutum 14 sun kamu a Najeriya, yanzu 288

0

Hukumar Hana Haduwar cututtuka ta kasa ta bayyana cewa mutum 14 sun kamu da cutar coronavirus ranar Alhamis.

Sakamakon gwajin da NCDC ta yi ya nuna cewa an samu karin mutum 14 daga jihohi 2 a kasar nan.

13 a jihar Legas, 1 a Delta.

Hukumar ta ce 51 sun warke, 7 sun rasu.

Legas -158

FCT – 54

Osun – 20

Oyo – 11

Akwa Ibom – 5

Ogun – 4

Edo – 12

Kaduna – 5

Bauchi – 8

Enugu – 2

Ekiti- 2

Ribas – 1

Benuwai – 1

Ondo – 1

Kwara – 2

Delta – 2

Katsina – 1

Idan ba a manta ba a wani labari ya auku a jihar Kaduna, Iyaye da ‘yan uwan wani matashi da ya dawo daga jihar Legas sun arce sun bar masa gida bayan ya dawo daga Legas a Unguwar Kurmi, karamar hukumar Igabi, jihar Kaduna.

Shi dai wannan matafiya, ya fara amai, da zazzabi mai zafi ne bayan dawowa daga Ikko, ganin haka kuwa sai ‘yan uwansa suka tattara nasu-ina su suka arce suka bar masa gidan.

Mai anguwan Kurmi Liman Hamisu, ya shaida wa manema labarai cewa daga baya sai mutanen gari suka fada cikin fargaba ganin yadda yan uwan wannan matashi suka kauce daga gidan, tsoron coronavirus.

Share.

game da Author