Gwamnan Bauchi Bala Mohammed ya warke daga cutar coronavirus da yake fama da shi.
Gwamna Bala ya bayyana haka a shafin sa na tiwita inda ya ke godewa Allah ya ce” Wannan shine karo na biyu da da aka yi min gwajin coronavirus aka samu ba ni dashi.
” In godewa Allah, na samu lafiya yanzu.”
A ranar litinin mataimakin gwamnan jihar, Baba Tela ya bayyana cewa gwajin da aka yi masa na coronavirus ya nuna baya dauke da cutar.
Idan ba a manta ba gwamna Bala na daga cikin wadanda suka kamu da cutar a jihar Bauchi.
Yanzu gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ne ya rage a killace ana duba shi cikin gwamnonin da suka kamu da cutar a Najeriya.