COVID-19: Likitoci uku sun kamu da cutar a jihar Legas

0

Kungiyar likitocin jihar Legas ta bayyana cewa likitoci 3 sun kamu da cutar Korona Baros a jihar.

Shugaban kungiyar Oluwajimi Sodipo da sakataren kungiyar Ismail Ajibowo suka sanar da haka ranar Alhamis.

Jami’an Kungiyar sun ce likitoci na aiki ne a asibitin koyarwa na Jami’ar jihar Legas da asibitin Alimosho.

A yanzu dai likitoci na samun magani a asibitocin kula da mutanen da suka kamu da cutar a jihar.

Oluwajimi Sodipo ya ce ma’aikatan kiwon lafiya sun fara neman mutanen da suka yi cudanya da lokitocin domin killace su da yi musu gwajin cutar.

Sodipo ya yi kira ga duk ma’aikatan kiwon lafiya da su guji duba mara lafiya ba tare da sun saka kayan samun kariya daga kamuwa da cutar ba.

Ya kuma ce Kungiyar su za ta tattauna da gwamnati domin tsara hanyoyi kare ma’aikatan kiwon lafiya da biyansu alawus domin karfafa gwiwowinsu a lokacin da suke aikin kula da masu fama da cutar a kasar nan.

Idan ba a manta ba a ranar Alhamis Ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya sanar cewa ma’aikatan kiwon lafiya 40 sun kamu da cutar Korona Baros a kasar nan.

Ehanire ya yi kira ga ma’aikatan kiwon lafiya da su tabbatar sun saka rigunar kare kai daga kamuwa da cutar kafin duba kowani mara lafiya a asibiti.

Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin wadanda suka kamu da cutar coronavirus a kasar nan ranar Alhamis.

A bayanan da NCDC ta fitar, Legas ta samu karin mutum 78, Abuja 15, Kwara 1, Ogun 5, Gombe 4, Barno 3, Akwa-Ibom 2, Filato 1.

Yanzu mutum 981 kenan suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 197 sun warke, 31 sun mutu.

Share.

game da Author