Idan ba a manta ba a ranar Alhamis ne hukumar NCDC ta sanar cewa cutar Covid-19 ta bullo a jihar Filato.
NCDC ta ce an gano cutar a jikin wata mata da tayi dakon ta daga jihar Kano ranar 17 ga watan Afrilu.
A ranar 23 ga watan Afrilu ne sakamakon gwajin da aka yi wa matan ya nuna cewa ta kamu da cutar.
Kwamishinan kiwon lafiya ta jihar Ninkong Ndam ya ce matar na asibitin kula da mutanen da suka kamu da cutar ana duba ta.
Yanzu mutum 981 ne suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 197 sun warke, 31 sun mutu.
Tun da cutar ta bullo a watan Fabrairu zuwa yanzu fannin kiwon lafiyar Najeriya ta yi wa mutum 9,522 gwajin cutar.
RUFE MAKARANTUN ALLO DA SAKA DOKAR ZAMAN GIDA DOLE
Domin hana yaduwar cutar gwamnati Filato za ta maida almajirai dake karatun allo a jihar zuwa jihohin su ta asali.
Duk gwamnoni Arewa sun amince da Wannan shiri domin kare almajirai daga kamuwa da cutar.
Gwamnati ta kuma ce ta janye dokar zaman gida dole a ranar 23 ga watan Afrilu. Sannan a ci gaba ranar 27 ga watan Afrilu.
Gwamnati ta ce hutun da gwamnati ta bada zai taimaka wa mutane siyan kayan abinci kafin dokar ta ci gaba da aiki.
Discussion about this post