An yi jana’izar mahaifiyar ministan ilmi, Adamu Adamu a Azare

0

A ranar juma’a ne aka sanar da rasuwar mahaifiyar ministan ilmi, Adamu Adamu, Fatima Adamu.

Kakakin ma’aikatar ilimi, Ben Gooong, ya fitar da sanarwar haka wadda minista Adamu ya saka wa hannu.

Marigayiya, Fatima ta rasu da safiyar ranar Juma’a, 1 ga watan Ramadan, 2020.

An yi jana’izarta a garin Azare, Jihar Bauchi kamar yadda shari’ar musulunci ya karantar.

Allah ya ji kanta, Amin.

Share.

game da Author