COVID-19 – Gwamnatin Gombe na Shirin Ko Ta Kwana

0

Gwamnati jihar Gombe ta bayyana cewa za ta hada hannu da hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa NCDC domin bude asibitin kula da masu fama da cutar coronavirus da wuraren yin gwajin cutar a jihar.

Gwamnan jihar Inuwa Yahaya ya sanar da haka wa manema labarai ranar Talata.

Yahaya ya ce gwamnati za ta yi haka ne domin dakile yaduwar cutar duk da cewa jihar Gombe na cikin jihohi 17 da cutar bata bullo ba a Najeriya.

Ya ce a ranar 23-ga watan Maris gwamnati ta kafa kwamitin mutum 23 domin tsara hanyoyin hana shigowa da cutar a jihar.

Ya ce kwamitin ta killace wasu asibitocin guda uku domin kula da wadanda suka kamu da cutar.

Sannan kwamitin na kokarin kara yawan asibitocin kula da masu fama da cutar a kananan hukumomin Funakaye da Kaltungo.

Yahaya ya ce kwamitin ta zuba kayan aiki da magunguna da Za a bukata da ya kai na Naira miliyan 200.

Ya ce an kuma horas da ma’aikatar kiwon lafiya kan dabarun gano cutar da yadda za su kula da wadannan suka kamu da cutar.

Sannan ma’aikatar kiwon lafiya ta fara wayar da kan mutane kan cutar da hanyoyi guje wa kamuwa da cutar.

Gwamna Yahaya ya ce gwamnati ta rufe duk makarantun boko, hana ma’aikatan gwamnati daga level 1 zuwa 12 zuwa aiki, rufe iyakolin jihar tare da hana taron mutane musamman na addinin da na kasuwanni a jihar.

Yahaya ya ce gwamnati Za ta yi amfani da jami’an tsoro domin tilasta mutane kiyaye dokar hana walwala da gwamnati ta saka.

Share.

game da Author