Coronavirus: Mutum 12 sun kamu a Kano, yanzu 407 a Najeriya

0

Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin wadanda suka kamu da cutar coronavirus a kasar nan ranar Talata.

A bayanan da ta fitar, Jihar Kano ta yakato akalla mutum 12, cikin mutum 34 da aka bayyana sun kamu a ranar talata.

Jihar Legas 18, Katsina 2, Neja 1, Delta 1 Kano 12.

Yanzu mutum 407 kenan suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 122 sun warke, 12 sun mutu.

Lagos- 232
FCT- 58
Osun- 20
Kano- 16
Edo- 15
Oyo- 11
Ogun- 9
Katsina- 7
Bauchi- 6
Kaduna- 6
Akwa Ibom- 6
Kwara- 4
Delta- 4
Ondo- 3
Enugu- 2
Ekiti- 2
Rivers-2
Niger- 2
Benue- 1
Anambra- 1

Ministan Harkokin Lafiya, Osagie Ehanire, ya shawarci jama’a su juri yin amfani da takunkumin rufe baki da hanci ko hankici ko wani dan kyalle su na rufe bakin su da hanci, domin rage yiwuwar kamuwa da cutar Coronavirus.

Ehanire ya yi wannan karin hasken ne a lokacin da ya ke amsa tambayoyi a ranar Litinin a Abuja.

Ya ce wadannan hanyoyi ne na rage yiwuwar kamuwa da cutar, musamman idan mutum ya shiga cikin Jama’a.

“Rufe hanci da baki da takumkumi ko hankici ko wani kyalle kan hana feshin miyau shiga hancin mutum, ko wani burtsatsin kwayoyin cuta daga bakin mai magana da karfi a kusa da mutum. Kai ko wani idan ya yi gwaron numfashi kusa da kai. Ko wanda ya balgace da dariya da karfi. Ko wanda ya hangame baki ya na magana da karfi.

“Daura wannan takunkumi na da amfani a inda shiga jama’a ya zama tilas, musamman a cikin kasuwa.

“Sai dai kuma saboda irin takunkumin da mu ke amfani da shi, wanda ake amfani da shi ne a rana tal. Ana jefar da shi a kwandon shara na da ya kwana daya.

” Amma wanda ya ga ba ya iya jefarwa ko kuma mai amfani da hankici ko wani dan kyalle, to ya rika wanke shi a kullum da yamma. Ya shanya shi, sannan ya goge shi da dutsen guga idan ya bushe.”

Kasuwar Wasu Za Ta Bude
Wannan kira da ya yi zai sa kasuwar amfani da hankici ta kara budewa kamar yadda ta bude a farkon watan Maris, musamman a Abuja da wasu garuruwa.

Kafin bayyanar cutar Coronavirus, ana saida takunkumin rufe hanci da baki naira 50 zuwa 100. Amma sai da ta kai ana sayen sa a kan titinan Abuja naira 500.

Idan ba a tuna ba, Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce babu wani tabbas wai takunkumin rufe hanci da baki na zama kariya daga kamuwa da cutar Coronavirus.

Share.

game da Author