COVID-19: An sallami mutum uku a Kaduna

0

Ma’aikatar kiwon Lafiya ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu mutum uku da ke kwance a dalilin kamuwa da Coronavirus a jihar.

Dama kuma can baya mutum shida ne aka kwantar a jihar sun kamu da cutar.

Yanzu mutum hudu kenan aka sallama daga asibiti. Saura mutum biyu.

Kwamishina Amina Baloni ta ce yanzu saura mutum biyu ke kwance ana duba su. Sannan kuma ta yi kira ga mutane da su rika kiyaye umarnin mahukunta da likitoci wajen kare kai da tsaftace jiki da muhalli.

” Rashin kamuwa da cutar ya fi sauki fiye da warkewa. Saboda haka kauce wa kamuwa da cutar shine mafita ga kowa da kowa.”

Share.

game da Author