Coronavirus ta ratsa kwamitin coronavirus na jihar Kano, mambobi 3 sun kamu

0

Kwamishinan kiwon lafiyar jihar Kano Hadiza Namadi,tabce mambobi uku na kwamitin dakike yaduwar cutar coronavirus a jihar sun kamu da cutar.

“A dalilin haka ya sa nake kira ga mutanen jihar su zauna a gidajen su. Sannan su rika nesa da juna. Sannan a rika wanke hannaye da tsaftace jiki.

Har zuwa ranar Juma’a da safe, mutane 21 ne suka kamu da cutar, sannan mutum daya ya rasu.

Sai dai kuma shugaban kwamitin cutar coronavirus na jihar Kano, kuma mataimakin gwamnan jihar Nasiru Gawuna ya bayyana cewa gwajin sa ya nuna bashi da cutar.

Daga nan sai ya yi kira ga mutanen jihar su kiyaye dokokin da gwamnati ta saka da kuma wanke hannaye da yin nesa-nesa da juna.

Idan ba a manta ba, a jihar Kaduna kuma, mutum hudu a ka sallama daga asibiti bayan sun warke daga cutar.

Yanzu saura mutum, biyu kacal da suka kamu da cutar.

Share.

game da Author