Kyamatar wadanda ke fama da Coronavirus na kawo mana cikas a aikin mu – NCDC

0

Shugaban hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) Chikwe Ihekweazu ya koka kan yadda mutane ke kyamatar wadanda suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya.

Ihekweazu ya fadi haka ne a zaman da kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar COVID-19 ya yi a Abuja ranar Alhamis.

Ya ce nuna wariya da ake yi wa wadannan ke dauke da cutar na dawo wa hukumar da hannun agogo baya a aiyukkan da suke yi na hana yaduwar a Najeriya.

Ihekweazu ya ce NCDC na kokarin ganin ta kara yawan mutanen da ake yi wa gwajin cutar a kasar nan amma hakan ba zai yiwu ba idan ana ana kyamatar su a duk inda suke.

Ya ce mutane za su fara guje wa yin gwajin cutar da boye wa ma’aikatan kiwon lafiya saboda haka.

Idan hakan ya fara faruwa a kasar nan cutar za ta ci gaba da yaduwa a kasar ba tare da sanin gwamnati ba.

“Kwanakin baya mun samu labarin cewa wasu masu dauke da cutar da aka kwantar a asibitin jihar Osun sun gudu saboda malaman asibitin dake duba su sun tafi sun barsu.

“Idan haka ya faru duk wanda ke dauke da cutar zai koma gida ya yadawa duk iyalensa da ‘yan uwa cutar kenan.

Ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya yi kira ga mutane da su guji nuna wa mutanen da suka kamu da cutar ko kuma suka warke daga cutar wariya.

Ehanire ya ce nuna wa mutane irin haka wariya zai hana mutane kiyaye hanyoyi guje wa kamuwa da cutar sannan ya hana a samu nasarar dakile yaduwar cutar a kasar nan.

A yanzu dai mutane 442 ne ke dauke da cutar a Najeriya, 153 sun warke sannan 13-sun mutu.

Share.

game da Author